Abinda Kashim Shettima, tsohon gwamnan Borno, ya fada a kan yi wa Buhari ihu a Maiduguri

Abinda Kashim Shettima, tsohon gwamnan Borno, ya fada a kan yi wa Buhari ihu a Maiduguri

Kashim Shettima, Sanata mai wakiltar jihar Borno ta tsakiya, yace har yanzu mutane na matukar son shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ya ce hakan ne washegarin ranar da jama’ar jihar Borno suka yi wa shugaban kasar ihun 'bama so' yayin ziyarar jaje da ta’aziyyar rayukan da aka rasa a harin da ‘yan Boko Haram suka kaiwa Auno.

A yayin zantawa da manema labarai a yau Alhamis, shettima ya kwatanta abinda ya faru da mara dadi kuma ba haka rai yaso ba.

Sanatan ya kara da cewa, mutane duk sun saka burikansu ne kan Buhari saboda suna zaton zai gyara kasar farat daya ne. "Jama’ar jihar Borno har yanzu suna son Buhari. Zai yuwu dai sunyi tsammani mai yawa ne. Ina da tabbacin cewa jama’ar Arewa maso gabas na kaunar Buhari. Da babu hadin kan jama’ar jihar Borno, ba za a samu ‘yan taimakon kai da kai ba.

“Jama’a da gwamnatin jihar Borno na goyon bayan shugaban kasa. Suna kuma jajanta yadda sojin Najeriya ke rasa rayukansu wajen tsaresu.

Shettima ya ce Buhari yana matukar damuwa da yadda koyaushe ake kai hare-hare a jihar.

“Za ta iya yuwuwa yayi magana ne da ta shafi kowa kuma wacce za ta hada kan jama’ar jihar, amma ina da tantama idan aka ce shugaban kasar ya dora laifin ta’addancin a kan jama’ar jihar Borno,” y ace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng