Majalisar Shari’a Ta Gaji da Ganin Yadda Aka Tsare El Rufai Ta Kai An Soma Magana
- Majalisar Shari’a ta jaddada cewa neman adalci dole ne ganin yadda shari’ar Nasir El-Rufai take tafiya
- Kungiyar ta nuna cewa tsare mutum ba tare da bin matakan doka na gaskiya ba yana keta hakkin dan-adam
- SCSN ta yi gargadin cewa matakin tsare tsohon gwamnan yana haifar da alamar tambaya game da shari’ar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Majalisar kolin shari’a ta Najeriya wato SCSN ta fito ta yi magana game da cigaba da tsare Nasir El-Rufai da ake yi har yau.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai yana hannun hukuma kusan tun bayan dawowarsa Najeriya daga Masar.

Source: Facebook
Shari'ar Nasir El-Rufai da ICPC da DSS
A makon nan Daily Trust ta rahoto cewa Majalisar SCSN ta nuna damuwa game da yadda ake shari’ar Nasir El-Rufai da ICPC.
ICPC tana zargin tsohon gwamnan da aikata laifuffuka tara da suka shafi kwangiloli, wanke kudin haram zuwa cin amanar ofis.
Baya ga ita ma hukumar DSS tana shari’a da shi bisa zargin yi wa Mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu kutse a waya.
El-Rufai: Jawabin Sakatare Janar na SCSN
SCSN ta fitar da jawabi ta bakin Sakatare Janar din ta, Malam Nafiu Baba Ahmad, tana bukatar a yi wa El-Rufai adalci a gaban kuliya.
Malam Nafiu Baba Ahmad ya ce kamar kowane ‘dan Najeriya, El-Rufai mai gaskiya ne har sai alkali ya same shi da aikata wani laifi.
Ya bukaci doka ta yi aiki a kan kowa a Najeriya ba tare da duba matsayinsa ba, tana cewa akwai alamar tambaya a shari’ar El-Rufai.
Majalisar ta tuna wa hukumomi cewa wajibi ne doka ta yi aiki kuma a saurari kowane bangare.
A matsayinta na kungiya mai goyon bayan adalci da gaskiya da bin doka, SCSN ta ce Najeriya na bin tsarin mulki na damukaradiyya ne.
Karkashin wannan tsari kuwa, kowane ‘dan kasa yana da hakkin a yi masa adalci ba tare da duba matsayi, akidar siyasa ko wani abu ba.

Source: Facebook
SCSN ba ta goyon bayan masu laifi
An rahoto a shafin The Nigerian Lawyer na malaman shari’a cewa SCSN ta kuma bayyana cewa ba ta goyon bayan aikata ba daidai ba.
Baba Ahmad ya fada wa hukumomin da ke shariar su tabbatar an yi abin da ya kamata saboda gudun a yi zargin an siyasantar da shari’ar.
Jawabin da Sakatare Janar ya fitar ta bukaci a yi adalci kuma duniya ta ga alamun hakan saboda a kare kima da martabar hukumomin kasa.
Mutuwar tsohuwa ya ba El-Rufai gajeren 'yanci
An ji labarin sakin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, daga hannun hukumar ICPC da aka yi bayan rasuwar mahaifiyarsa kwanaki.
Bashir El-Rufai (ɗan tsohon gwamnan) ya sanar a shafinsa na X (Twitter) cewa an saki mahaifinsa daga tsarewar da hukumar ICPC ta yi masa a Abuja.
Hakan ya faru ne sa'o'i kadan bayan rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Umma a watan Maris. Daga baya dai ya sake koma wa hannun hukumomin gwamnati.
Asali: Legit.ng

