Nafiu Bala Ya Kawo Sabon Rikici a ADC kan Yadda Atiku ke Sukar Tinubu

Nafiu Bala Ya Kawo Sabon Rikici a ADC kan Yadda Atiku ke Sukar Tinubu

  • Rahotanni sun nuna cewa jam’iyyar ADC ta yi Allah-wadai da abin da ta kira amfani da sunanta, tambarinta da alamominta ba bisa izini ba
  • Tsagin Nafiu Bala na jam’iyyar ya zargi tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da yin ayyukan da ya ce suna barazana ga Najeriya
  • ADC ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, 31 ga Agusta, 2026, bayan wani taron gaggawa na kwamitin amintattu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Jam’iyyar ADC tsagin Nafiu Bala ta yi kakkausar suka ga abin da ta bayyana a matsayin amfani da sunan jam’iyyar da tambarinta ba bisa izini ba, tana mai cewa hakan na iya jefa Najeriya cikin abin kunya a idon ƙasashen duniya.

Kara karanta wannan

Atiku ya ragargaji Tinubu kan tafiya hutu Turai 'Najeriya na ci da wuta'

Jam’iyyar ta kuma yi zargin cewa Atiku Abubakar na ƙoƙarin amfani da sunan ADC wajen aiwatar da abin da ta kira daukar fansa na siyasa da kuma ayyukan da za su iya jefa Najeriya cikin abin kunya a duniya.

Nafiu Bala, David Mark da Atiku Abubakar
Shugaban ADC, Davd Mark, Nafiu Bala da Atiku Abubakar. Hoto: ADC Vanguard|Nafiu Bala
Source: Twitter

Legit Hausa ta tattaro bayanin da Nafiu Bala ya yi ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a daren Litinin, 31 ga Agustan 2026.

Nafiu Bala ya soki Atiku

A cikin sanarwar da shugaban ADC na ƙasa, Hon. Nafiu Bala, ya sanya wa hannu, jam’iyyar ta ce ta umarci a dakatar da duk wani amfani da sunanta, tambarinta da alamominta ta hanyar bogi ko ba tare da izini ba.

Ta ce ba za ta amince da amfani da sunanta wajen yada abin da ta kira ƙaryace-ƙaryace ko kunyata Najeriya a gaban ƙasashen duniya ba.

ADC ta ce irin waɗannan matakai na iya rage martabar Najeriya a tsakanin ƙasashen duniya, tare da bayyana ƙasar a matsayin wadda ba ta da bin doka.

Jam’iyyar ta kuma ce duk wani ƙorafi da ake da shi kan Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya kamata a gabatar da shi ta hanyoyin doka da cibiyoyin Najeriya.

Kara karanta wannan

Kirista ya lashe gasar Kur'ani, ya samu kyautar kujerar Umrah

ADC ta ce tana sanar da Atiku Abubakar cewa ya daina gabatar da kansa ko magana a madadin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar.

Maganar hadakar 'yan adawa

Dangane da batun ƙungiyar G100 Coalition, ADC ta ce shugabancinta na sane da matsin lamba da wasu mutane ke yi, da kuma tattaunawar da ake gudanarwa a ɓoye da nufin tilasta jam’iyyar shiga wata ƙawance ko haɗaka.

Jam’iyyar ta bayyana a sarari cewa ba ta cikin wata ƙawance, haɗaka ko haɗin gwiwa da wata jam’iyyar siyasa gabanin zaɓen 2027, tana mai cewa za ta tsaya takara da kanta.

Nafiu Bala da kakakn ADC
Nafiu Bala a hagu da kakakin ADC a dama. Hoto: Nafiu Bala|Bolaji Abdullahi
Source: Facebook

Nafiu Bala ya ce ADC jam’iyya ce mai cin gashin kanta wadda za ta nemi nasara a zaɓe bisa akidar ta, tsarin ta da kuma amincewar al’ummar Najeriya.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta sake gano lam'a a shirin Atiku na dawo da tallafin fetur

Atiku Ya soki hutun Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC a 2027, Atiku Abubakar, ya soki Shugaba Bola Tinubu kan tafiyar da ya yi zuwa Turai.

Atiku ya ce tafiyar Tinubu a lokacin da Najeriya ke fuskantar matsalolin tattalin arziki da tsaro na nuna abin da ya kira “gurbin shugabancin siyasa mai tayar da hankali”.

Ya amince cewa babu gurbin shugabanci a tsarin kundin tsarin mulkin ƙasa, amma ya ce yanayin tafiyar shugaban ya haifar da tambayoyi kan abubuwan da ya fi bai wa muhimmanci a shugabanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng