Atiku ko Obi: Yan Adawa Sun Fara Daukar Matsayan da Za Ta Iya Kayar da Tinubu a Zaben 2027
- Dan takarar shugaban kasa na PRP, Donald Duke, ya yi alkawarin goyon bayan duk dan takarar da hadakar yan adawa ta tsaida a 2027
- Tsohon gwamnan Cross River ya ce zai ci gaba da goyon bayan tsarin hada kan ’yan adawa ko da tattaunawar jam’iyyun ba ta kasance yadda ake fata ba
- Kungiyar G-100 ta ce rarrabuwar kawuna ce ta taimaka wajen kayar da ’yan adawa a zaben shugaban kasa na 2023
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Dan takarar shugaban kasa na PRP, Donald Duke, ya yi alkawarin goyon bayan duk wani dan takarar ’yan adawa da zai fito daga kokarin da ake yi na kulla kawance gabanin babban zaben 2027.
Duke ya bayyana hakan ne ranar Litinin a taron G-100 Summit na jam’iyyun adawa na Najeriya da aka gudanar a Abuja.

Kara karanta wannan
Magana ta fito: Atiku ya bayyana dalilin da ya sa yake son dawo da tallafin fetur

Source: Facebook
Donald Duke ya shirya hadaka
Daily Trust ta ce tsohon gwamnan jihar Cross River ya ce zai ci gaba da jajircewa wajen ganin an hada kan ’yan adawa ba tare da la’akari da sakamakon tattaunawar da jam’iyyun da ke shirin za su yi ba.
“Za mu goyi bayan duk jam’iyyar siyasa da muka amince a marawa baya a 2027. Duk shawarar da aka cimma a yau, ba zan ja da baya ba, sai dai in ci gaba da kokari saboda abin da al’umma ke son gani ke nan,” in ji Duke.
Taron wanda G100 ta shirya tare da hadin gwiwar tsagin adawa a Majalisar Wakilan Tarayya, ya hada shugabanni da ’yan takarar jam’iyyun adawa shida.
Kungiyar G-100 ta bukaci hadin kai
A jawabin bude taron da ya gabatar a madadin G100, Mallam Salihu Lukman, ya ce ’yan adawa za su iya kalubalantar jam’iyyar da ke mulki yadda ya kamata a 2027 ne kawai idan suka hada kai.
A cewarsa, ya zama dole yan adawa su shawo kan rabuwar kawunan da ta taimaka wajen kayar da su a zaben shugaban kasa na 2023 idan suna son nasara a zabe mai zuwa.
Abin da ya hana kayar da APC a 2023
Lukman ya ce jam’iyyun adawa gaba daya sun samu kusan kuri’u miliyan 13 a zaben 2023, idan aka kwatanta da kasa da kuri’u miliyan 9 da wanda ya lashe zaben ya samu.
“Babu wanda ya sace kuri’u miliyan 13. Mu ne muka raba su da kanmu, a bainar jama’a, kuma mun yi hakan ne alhali muna sane da sakamakon da hakan zai haifar,” in ji shi.
Ya tuna da kawancen ’yan adawa da aka yi a zaben 2015, lokacin da jam’iyyun adawa suka tattauna sharuddan hadin gwiwa tare da amincewa da tsarin samar da dan takara guda kafin a yanke shawarar wanda zai rike tikitin.

Source: Twitter
A cewarsa, babban darasin da aka koya daga abin da ya faru a 2015 shi ne, ya kamata jam’iyyun adawa su fara amincewa da ka’idojin hadin gwiwa kafin su fara tattaunawa kan mukamai, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Peter Obi ya dura kan Tinubu
An ji cewa Peter Obi ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya yi wa ’yan Najeriya cikakken bayani kan wasu batutuwan da suka shafi tarihinsa, musamman karatunsa.
Obi ya ce ’yan Najeriya sun cancanci samun amsoshi kan batutuwan da suka shafi al’umma, musamman a daidai lokacin da ake samun rahotannin cewa shugaban kasar na kokarin hana bayyana gaskiya a kotun Amurka.
Asali: Legit.ng

