Sanata Ndume ya roki Buhari da ya kawo karshen rikicin Boko Haram

Sanata Ndume ya roki Buhari da ya kawo karshen rikicin Boko Haram

Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin sojoji, Sanata Ali Ndume, ya jadadda bukatar a gudanar da bincike kan harin da yan ta’adda suka kai Auno wanda ya yi sanadin mutuwar akalla mutane 30.

Ya ce bala'in da rikicin Boko Haram ya jefa jama’ar yankin arewa maso gabas musamman ma jahar Borno, ya isa haka nan inda ya yi kira ga gwamnati ta dauki matakin kawo karshensa.

Harin da yan ta’addan suka kai Auno na daya daga cikin hare-hare mafi muni da aka kai a baya-baya nan.

Mayakan sun kai harin ne da yayin da matafiyan ke barci cikin motocinsu bayan jami'an tsaro sun hana shiga birnin Maiduguri daga misalin karfe biyar na yammaci.

Ndume wanda shine ke wakiltar Borno ta kudu a majalisar dattawan ya ce "akwai sakaci, don haka nake goyon bayan kiran da Kashim Shetima ya yi cewa ya kamata a gudanar da bincike.”

Sanatan ya kuma roki gwamnati ta taimaka wa wadanda suka yi hasara harin da aka kai a Auno.

Sanata Ndume ya roki Buhari da ya kawo karshen rikicin Boko Haram
Sanata Ndume ya roki Buhari da ya kawo karshen rikicin Boko Haram
Asali: UGC

Har ila yau Ndume ya yi kira ga shugaban kasa da jami'an tsaro su tausayawa mutanen Borno a kawo karshen rikicin da ya ce ya addabi Borno tsawon shekaru 10.

"Don Allah muna rokon gwamnati ta taimaka ta kawo karshen wannan matsalar ko da kuwa sojojin haya za ta dauko ta shigo da su Borno, idan zai taimaka a kawo karshen rikicin.

"Muna nan muna binne mutanenmu ana muna barna kuma gwamnati tana da dama za ta iya magance wannan matsalar da ta addabe mu shekaru 10," in ji shi.

Da farko dai mun ji cewa tsohon gwamnan jahar Borno, kuma wakilin mazabar Bornon ta tsakiya a majalisar dattawa, Sanata Kashim Shettima ya yi kira ga shelkwatar tsaro ta Najeriya da ta gudanar da cikakken bincike game da harin Auno, domin kuwa akwai tambayoyi dake bukatar amsoshi game a harin.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya fi kowa fahimtar matsalar tsaron da Najeriya ke fama da shi – Buratai

Shettima ya bayyana haka ne cikin wata gajerar sanarwa daya wallafa a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Facebook da yammacin Talata, 11 ga watan Feburairu, inda yace tabbas an samu karuwar hare haren Boko Haram a yan kwanakin nan a wasu sassan jahar Borno.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel