Neman a sauya salon tsaron kasar: Kungiyar gwamnoni ta yaba ma Zulum

Neman a sauya salon tsaron kasar: Kungiyar gwamnoni ta yaba ma Zulum

- Kungiyar gwamnonin Najeriya ta mika sakon jaje zuwa ga mutane da gwamnatin jahar Borno kan harin Auno

- Kungiyar ta kuma yaba ma gwamnan jahar Borno, Babagana Zulum, kan kira ga sauya salon tsaron kasar baki daya

- An aika wasikar me a ranar 11 ga watan Fabrairu dauke da sa hannun Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriyan, Gwamna Kayode Fayemi na jahar Ekiti

Kungiyar gwamnonin Najeriya ta yaba ma gwamnan jahar Borno, Babagana Zulum, kan kira ga sauya salon tsaron kasar baki daya.

Kungiyar a wata wasikar jaje zuwa ga gwamnan, ya nuna bakin ciki da alhini kan harin ranar Asabar da ya gabata a garin Auno da ke jahar Borno, wanda a cikinta aka yi asarar rayuka da dukiyoyi.

An aika wasikar me a ranar 11 ga watan Fabrairu dauke da sa hannun Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriyan, Gwamna Kayode Fayemi na jahar Ekiti.

Neman a sauya salon tsaron kasar: Kungiyar gwamnoni ta yaba ma Zulum
Neman a sauya salon tsaron kasar: Kungiyar gwamnoni ta yaba ma Zulum
Asali: Depositphotos

Wasikar da suka aike wa Zulum ya zo kamar haka: “Ni Dr John Kayode Fayemi, gwamnan jahar Ekiti kuma shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, ina mika ta’aziyya a madadin gwamnonin kasar 36 kan harin da aka kai kan matafiya a karshen makon da ya gabata a garin Auno wajen babbar birnin jahar, Maiduguri.

“Yayinda muke taya ka alhini, ya mai girma, kungiyar na fatan bayyana cewa a lamarin da zai kai ga yan ta’adda su kawo motoci su cika shi da kayayyakin amfani sannan su cinna wa gidaje da shaguna wuta da kai hari kan matafiya masu bacci a garin da ke kilomita 24 daga babbar birnin jahar, ya nuna hatsarin da mutanen yankin ke ciki alhalin ya kamata a ce suna samun cikakken kariya daga mutanen da suka daura kan mulki.

“Don haka kokarinka na kira ga sauya fasalin tsaro a Fadin kasar abun a yaba ne, da kuma nuna jajircewa.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya yi martani a kan ihun da aka yi masa a Maiduguri

“A karo na biyu dani da takwarorina muna taya mutane da gwamnatin jahar Borno alhinin wannan ibtila’i sannan muna fatan za a ba mutane kariya don ganin irin haka bai sake faruwa ba bawai a jahar Borno ba kadai harma ga kasar baki daya.

“Dan Allah ku amshi jajenmu.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel