'Yan Adawa Sun Fitar da Tsarin Kafa Gwamnati a 2027 da Kifar da Tinubu

'Yan Adawa Sun Fitar da Tsarin Kafa Gwamnati a 2027 da Kifar da Tinubu

  • Shugabannin manyan jam’iyyun adawa shida sun gudanar da wani taro a Abuja domin ƙarfafa shirin haɗin gwiwa da nufin kayar da Bola Tinubu a zaɓen 2027
  • Taron ya gabatar da tsarin gwamnatin ƙasa da wa’adin mulki guda ɗaya na shekaru huɗu, yayin da manyan ’yan siyasa ba su halarta ba
  • Daya daga cikin jagororin 'yan adawa, Salihu Lukman ya yi karin bayani game da abubuwan da suka sa a gaba da yadda suke son cimma su a zabe mai zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Shugabannin manyan jam’iyyun adawa shida a Najeriya sun taru a Abuja domin ƙulla tsarin haɗin gwiwa da nufin kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Sai dai ’yan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar; Peter Obi na NDC; da Seyi Makinde na Oyo da ke APM, ba su halarci taron ba.

Kara karanta wannan

'Yan adawa za su yi babban taro a yau domin shirin kifar da Tinubu a 2027

Wajen taron 'yan adawa
Wakilan jam'iyyu a wajen taron 'yan adawa na G-100 a Abuja. Hoto: ADC Voice
Source: Facebook

Vanguard ta ce taron ya samu halartar wasu ’yan takarar shugaban ƙasa da mataimakansu, ciki har da Adewole Adebayo na SDP, Donald Duke na PRP da mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na APM, Lawal Musa Daura.

Tsarin da 'yan adawa suka kawo

A jawabinsa na buɗe taron a madadin G-100, Malam Salihu Lukman ya gabatar da tsarin kafa gwamnatin kasa, wadda za ta kasance ƙarƙashin wa’adin mulki guda ɗaya na shekaru huɗu.

Lukman ya ce tsarin zai mayar da hankali kan ƙwarewa, gaskiya, haɗa kan ƙasa da kuma bai wa kowace jam’iyyar da ta shiga ƙawancen damar wakilci mai adalci.

Ya ce wa’adin shekaru huɗu ɗin zai kasance cikin wata yarjejeniyar sauyin mulki da za a iya aiwatar da ita bisa doka.

“Wannan taro ba ya neman wata jam’iyya ta rushe. Ba ya neman wata jam’iyya ta shiga cikin wata jam’iyya. Ba ya neman wani ɗan takara ya janye a safiyar yau,”

Kara karanta wannan

Atiku ya ragargaji Tinubu kan tafiya hutu Turai 'Najeriya na ci da wuta'

In ji shi.

Batun kwamitocin haɗin gwiwa

Punch ta wallafa cewa Lukman ya bayyana cewa ana shirin kafa kwamitocin haɗin gwiwa guda uku domin tafiyar da aikin ƙawancen.

Ya ce kwamitin farko zai ƙunshi shugabannin jam’iyyu na ƙasa, sakatarorin ƙasa da ’yan takarar shugaban ƙasa da mataimakansu domin samar da jagorancin siyasa.

Manyan 'yan adawa a Najeriya
Atiku Abubakar da wasu 'yan adawa a wajen zanga-zanga. Hoto: Mr Peter Obi
Source: Facebook

Sauran kwamitocin za su kula da yaɗa manufofin haɗin gwiwar da sadarwa, da kuma dabarun shari’a da shawarwari kan batutuwan ƙawancen.

Tsagin ADC ya soki Atiku

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsagin jam’iyyar ADC ya soki tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, kan kai ƙarar Shugaba Bola Tinubu zuwa kotunan ƙasashen waje.

Shugaban ADC na ƙasa, Hon. Nafiu Bala Gombe, ya ce duk wani ƙorafi da ake da shi kan shugaban ƙasa ya kamata a gabatar da ita cikin tsarin dokokin Najeriya da cibiyoyinta.

Jam’iyyar ta bayyana kai ofishin shugaban ƙasa zuwa kotun ƙasar waje a matsayin abin da ta kira “rashin kishin ƙasa” da kuma barazana ga tsaron ƙasa da muradun Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng