Ranar da Tsohon Gwamna Ya Bar APC, EFCC Ta Tado Zancen Neman Sa kan Zargin Satar $14m
- Hukumar EFCC ta jaddada cewa har yanzu tana neman Timipre Sylva ruwa a jallo domin ya amsa tambayoyi
- Tsohon ministan man ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar APC yayin da ya zargi APC da karya alkawuran da ta yi
- Ganin Sylva ya aika da takardar murabus dinsa zuwa EFCC, an tuna masa ana zarginsa da karktar da $14m
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Hukumar EFCC mai yaki da rashin gaskiya, tana neman Timipre Sylva ruwa a jallo saboda zargin satar kudi.
Ana tuhumar tsohon gwamnan na jihar Bayelsa da satar $14.86m don haka EFCC ta bukaci ya kawo kan shi da kan shi.

Source: UGC
Ana neman Timipre Sylva a ofishin EFCC
Rahoto ya fito daga jaridar Punch cewa an bukaci ‘dan siyasar ya kai kan shi gaban hukumar domin ya amsa tambayoyi.
Kakakin EFCC na kasa, Dele Oyewale ya bayyana wannan a ranar Litinin a kokarin maida wa tsohon gwamnan martani.
Timipre Sylva ya zargi hukumar yaki da rashin gaskiyar da zama tamkar wani bangare na jam’iyyar APC mai mulki a kasa.
Hikumar EFCC tana neman Sylva har gobe
Mista Dele Oyewale ya shaida wa duniya cewa yanzu haka aka neman Cif Sylva kuma ana bukatar ya kawo kan shi hedikwatar EFCC.
Da ya tashi barin APC, ‘dan siyasar ya rubuta a takardar murabus dinsa cewa jam’iyyar da su ne suka kafa ta, ta saki layi a halin yanzu.
Sannan kuma ya hada da EFCC a wasikar, yana sanar da ita wannan mataki da ya dauka.
Wasikar tsohon gwamnan ta tsokano EFCC
Ko da aka nemi jin dalilin ambatar hukumar EFCC a wasikar da ya fitar, Jaridar The Sun ta rahoto shi yana cewa da gan-gan da ya yi hakan.
Ana zargin hukumomin yaki da rashin gaskiya da siyasantar da binciken da suke yi a Najeriya.

Source: Getty Images
Tsohon karamin ministan na harkokin man fetur ya kuma ce yana sane cewa barin jam’iyyar zai iya jefa shi da yaransa na siyasa a matsala.
Duk wannan abin da aka yi har ake zarginsa da hannu a shirya wa gwamnatin Bola Tinubu juyin mulki, ‘dan siyasar yana kasar waje.
Sai dai duk da yiwuwar bita-da-kullin, Cif Sylva ya yi sallama da jam’iyyar APC mai-ci.
APC ta rasa tsohon gwamnan Bayelsa
Tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Timipre Sylva, ya sanar da murabus dinsa daga jam’iyyar APC mai mulki ba tare da wani bata lokaci ba.
Sylva ya bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne saboda yadda jam'iyyar ta karkata daga manufofi da akidojin da aka kafa ta a kansu.
Da alama dai murabus dinsa na zuwa ne sakamakon zargin da ake yi masa na hannu a shirin juyin mulki da kuma zargin karkatar da kudi
Asali: Legit.ng

