Yan siyasa ne suka biya ‘zauna gari banza’ don su yi ma Buhari ihu a Borno – Garba Shehu

Yan siyasa ne suka biya ‘zauna gari banza’ don su yi ma Buhari ihu a Borno – Garba Shehu

Babban hadimin shugaban kasa a kan harkokin watsa labaru, Malam Garba Shehu ya bayyana cewa wasu yan siyasa ne suka dauki nauyin biyan yaransu yan bangan siyasa domin su yi ma shugaban kasa Muhammadu Buhari ihu a jahar Borno.

A yayin ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai jahar Borno ranar Laraba domin jajanta ma al’ummar jahar biyo bayan hare haren Boko Haram ne jama’an da suka saba fitowa tarbar shugaban a baya suka koma suna koma suna masa ihun ‘Bama so’.

KU KARANTA: Hukuma ta yi kwarmato game da shirin kai ma majalisa harin ta’addanci

TheCables ta ruwaito cikin wata hira da ya yi da BBC Hausa, Garba Shehu ya bayyana cewa yan barandan siyasa ne kawai suka yi ma shugaba Buhari ihu.

“Ina cikin tawagar shugaban kasa da suka shiga Maiduguri tun daga filin sauka da tashin jirage har zuwa fadar mai martaba Shehun Borno, jama’a sun fito sun yi ta maraba da zuwanmu suna mana godiya.

“Amma akwai wasu gungun jama’a da suka fito suna ihun ‘Ba ma so’ wasu yan siyasa ne suka tarasu suka biyasu kudi domin su yi ma Buhari ihu.” Inji shi.

Sai dai Malam Garba ya ce gwamnatin shugaba Buhari na da karfin yaki da Boko Haram. Amma a yayin ziyarar, an jiyo gwamnan jahar Borno, Babagana Umara Zulum yana shaida ma shugaban kasa cewa akwai bukatar Sojoji su canza salon yaki da Boko Haram.

Zulum ya bada shawarar kamata ya yi Sojoji su dinga bin yan ta’addan Boko Haram har inda suke sansani.

A wani labarin kuma, hukumar majalisar dokokin Najeriya ta bayyana damuwarta game da yiwuwar kungiyar ta’adda ta kaddamar da harin ta’addanci a majalisa, kamar yadda wani babban jami’in hukumar ya bayyana.

Wannan jami’I da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa: “Da gaske ne, mun samu mummunan rahoton tsaro dake bayyana cewa majalisar dokokin Najeriya na daga cikin wuraren da yan ta’adda ke shirin kaddamar da hari, kuma ba na wasa bane.”

Jami’in yace suna yawan samun bakin fuskoki dake shiga cikin majalisa a yan kwanakin nan, kuma hakan ya zama abin damuwa ga hukumar majalisar, kamar yadda ya shaida ma majiyar Legit.ng.

Jami’in ya kara da cewa a lokutta da dama da zarar jami’an hukumar ko jami’an tsaro sun tunkari wadannan bakin fuskoki game da dalilin zuwansu majalisar sai su ce sun zo wurin wakilansu ne, bugu da kari jami’an tsaron majalisar sun yi karanci.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel