Buhari ya yi martani a kan ihun da aka yi masa a Maiduguri

Buhari ya yi martani a kan ihun da aka yi masa a Maiduguri

Fadar shugaban kasa ta yi martani a kan ihun da wasu mutane suka yiwa shugaban kasa Muhammnadu Buhari a lokacin da ya kai ziyarar jaje a garin Maiduguri, babbar birnin jahar Borno.

Mai magana da yawun Shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya bayyana cewa wanda ya dauki wannan bidiyo na ihun da aka yi wa Shugaban kasar har ya yada shi bai yi wa mutanen jahar Borno adalci ba, shafin BBC ta ruwaito.

A cewarsa an san mutanen Borno da karamci da son baki.

Buhari ya yi martani a kan ihun da aka yi masa a Maiduguri
Buhari ya yi martani a kan ihun da aka yi masa a Maiduguri
Asali: UGC

Ya ce: “Da ni aka ziyarci Maiduguri tun daga filin jirgin sama har zuwa fadar Shehun Borno Sannan jama’a sun fito suna ta san barka.

“Sai dai akwai wata matattara da suka ce ba sa so, nima na ji da kunne na masu cewa ba sa so.”

Garba ya yi zargin cewa babu mamaki wasu yan adawa ne suka taro wasu yan tairaru suka cika su da kudi domin su yi wa shugaban kasar ihu.

Ya kara da cewa a gari irin Maiduguri, ba zai yiwu a ce an rasa mutanen da suka kai miliyan hudu zuwa biyar ba sannan cewa tunda mutum ba Allah ba ne ba shi yiwuwar a ce zai gamsar da kowa.

Ya ce gwamnatin Buhari ta nuna za ta iya yaki da Boko Haram kuma shugaban ya yi alkawalin canza matakan yaki na magance abin da ya kira sabuwar matsalar da aka samu.

KU KARANTA KUMA: Ta bayyana: Gaskiyar dalilin da yasa Kwankwaso da Abba gida-gida basu tarbi masoyinsu da ya yi tattaki daga Katsina ba

Harin da aka kai Auno ya fusata mutanen Borno, inda da dama suka zargi jami'an tsaro da sakaci bayan sun rufe hanyar shiga Maiduguri da yammaci, dalilin da ya sa mayakan Boko Haram suka riske matafiya a cikin dare.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo kasar bayan halartan taron AU na 33 a kasar Habasha.

Legit.ng ta rahoto cewa babban mai ba Shugaban kasa shawara kan kafofin watsa labarai, Garba Shehu ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Laraba, 12 ga watan Fabrairu.

Ya ce Shugaba Buhari, ya taso daga Addis Ababa sannan a yanzun nan ya sauka a Maiduguri, babbar birnin jahar Borno.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel