Hukuncin kotun koli: Masoya PDP sun shiga shaukin murna, sun yaga tutar APC

Hukuncin kotun koli: Masoya PDP sun shiga shaukin murna, sun yaga tutar APC

Magoya bayan jam’iyyar PDP a jihar Bayelsa sun fada shauki da murnar soke zaben jam’iyyar APC tare da dan takararta da kotun koli ta yi a yau. Alkalai biyar din na kotun, wadanda suka samu jagorancin Mai shari’a Mary Odili ne suka soke zaben sakamakon ikirarin rashin cancantar abokin tafiyar Lyon din. An zargesa da mikawa hukumar zabe mai zaman kanta ne takardun shaidar kammala karatu na bogi don tantancewa a zaben 16 ga watan Nuwamba.

Da wannan hukuncin na kotun, dan takarar jam’iyyar PDP a zaben, Diri Duoye ne za a rantsar da shi a gobe Juma’a bayan da ya bayyana a mai kuri’ar da ke biye da Lyon.

Gidan talabijin din Channel ta wallafa bidiyon magoya bayan jam’iyyar PDP a jihar Bayelsa din inda suke ta kida da rawa cike da nishadi a ofishin jam’iyyar da ke Yenagoa.

Har ila yau, a bidiyon dai an nuna cincirondon jama’a a gidan gwamnatin jihar Bayelsa din suna shagalinsu na murna. An dauka wasu kuma suna faman yaga tutocin jam’iyyar APC a jihar.

Hukuncin kotun koli: Masoya PDP sun shiga shaukin murna, sun yaga tutar APC
Hukuncin kotun koli: Masoya PDP sun shiga shaukin murna, sun yaga tutar APC
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Kotun koli ta kwace kujerar gwamnan APC David Lyon, ta bawa PDP

Shi kuwa Atiku Abubakar, a yayin mayar da martani a kan hukuncin kotun kolin, y ace “ya yi kira ga jama’ar jihar Bayelsa da su hada kansu wajen mayar da jihar Bayelsa ‘Aljannar duniya’.

Ya kara kira ga kotun kolin da ta cigaba da jajircewa wajen zartar da hukuncin tare da kawo mafita ga ‘yan Najeriya ba tare da duban wanda abin zai shafa ba. Kamar yadda ya wallafa, “Na samu labarin hukuncin kotun koli inda ta bayyana dan takarar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Bayelsa din. Nayi matukar farin ciki da jin cewa Sanata Duoye Diri ne halastaccen gwamnan jihar Bayelsa.”

“Ina kira ga jama’ar jihar Bayelsa da su zauna lafiya tare da rungumar junansu don mayar da jiharsu ‘Aljannar duniya’. Daga karshe ina kira ga kotun kolin da ta ci gaba da jajircewa wajen zartar da hukunci tare da kawo mafita ga ‘yan Najeriya ba tare da duban wanda abin zai shafa ba.” Ya wallafa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel