Shugaban Sojojin Amurka Ya Yi Murabus da aka Dawo Gwabza Yaki da Iran
- Shugaban sojojin kasan Amurka, Daniel Driscoll, ya gabatar da takardar murabus dinsa bayan tsawon watanni ana samun rashin jituwa da ministan tsaro, Pete Hegseth
- Fadar White House ba ta musanta rahoton murabus din Driscoll ba, yayin da wasu rahotanni suka ce har yanzu ba a tabbatar ko an amince da murabus din ba
- Driscoll ne sabon babban jami'in ma'aikatar tsaro da ya bar mukaminsa tun bayan da Hegseth ya karɓi jagorancin ma'aikatar bayan zuwan Donald Trump
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Washington DC – Shugaban Sojojin Kasa na Amurka, Daniel Driscoll, ya gabatar da murabus dinsa bayan watanni ana samun takun saka da ministan tsaron Amurka, Pete Hegseth.
Rahotonni da suka fito daga Amurka sun nuna cewa murabus din Driscoll ya fito ne a ranar Litinin, inda Fadar White House ta ki musanta shi.

Source: Getty Images
White House ta yabi Driscoll
Al Jazeera ta wallafa cewa kakakin fadar White House, Anna Kelly, ta bayyana cewa Driscoll ya taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da manufofin Shugaba Donald Trump a Ma'aikatar Sojojin Kasa.
Ta ce ya bayar da jagoranci a wasu muhimman ayyukan soji, ya mayar da hankali kan shirye-shiryen soji da karfin amfani da makamai, tare da taimakawa wajen tattaunawar kawo karshen yakin Rasha da Ukraine.
“Rundunar Sojojin Kasa ta Amurka ta fi karfi fiye da kowane lokaci saboda aikinsa tare da Babban Kwamandan Sojoji da Ministan Yaki,”
in ji Kelly.
Sai dai Reuters ta ruwaito cewa wata majiya mai masaniya kan lamarin ta ce har yanzu ba a san ko Fadar White House ta amince da murabus din Driscoll ba.
A daya bangaren kuma, Rundunar Sojojin Kasa ta Amurka ta ki cewa komai kan rahoton.

Source: Getty Images
Rikici tsakanin Driscoll da Hegseth

Kara karanta wannan
Manyan dalilai 4 da suka sa Tinubu yake neman kotu ta hana FBI sake sirrinsa na Amurka
Wata majiya ta shaida cewa Driscoll ya bayyana damuwarsa ga gwamnatin Trump kan sauye-sauyen da ake kokarin yi wa rundunar Sojojin Kasa da kuma shirye-shiryenta na yaki.
Majiyar ta ce Driscoll ya kuma nuna damuwa kan abin da ta kira hana Hegseth wadannan sauye-sauye, musamman ta hanyar korar manyan hafsoshin soji da ke da alhakin aiwatar da su.
BBC ta wallafa cewa Driscoll ya samu amincewar Majalisar Dattawan Amurka a watan Fabrairun 2025 domin zama Shugaban Sojojin Kasa, inda ya matsa wajen ganin rundunar ta fi saurin sayen makamai masu rahusa.
Ya kuma soki manyan kamfanonin kera makamai, yayin da babban aikinsa a matsayin shugaban sojojin kasa ya hada da kula da horar da sojoji da samar musu da kayan aikin da suke bukata.
Iran ta kai wa Amurka hari
A wani labarin, mun ruwaito cewa Rundunar Sojin Iran ta sanar da kai hari kan sansanin sojin Amurka da ke Al Minhad a Hadaddiyar Daular Larabawa da jiragen sama marasa matuka masu kunar bakin wake.
Rahotanni sun nuna cewa rundunar ta ce jiragen sun kai hari kan wuraren da ke dauke da sojojin Amurka da jirage masu saukar ungulu a sansanin.
Iran ta bayyana harin a matsayin martani kai tsaye ga harin da Amurka ta kai ranar Lahadi a tsibirin Larak da ke kudancin Iran, wanda majiyoyin Iran suka ce ya kashe mutum biyu tare da jikkata wasu.
Asali: Legit.ng
