"Gwamnatin Mu Ce"; Kwamishina Ya Yi Barazanar Karya 'Yan Yatsun Masu Adawa da APC

"Gwamnatin Mu Ce"; Kwamishina Ya Yi Barazanar Karya 'Yan Yatsun Masu Adawa da APC

  • Kwamishinan Borno Sainna Buba ya yi barazanar cutar da masu sukar APC, yana cewa za a “karya yatsunsu” idan suka nuna adawa
  • Buba ya ce masu goyon bayan gwamnati za su more amfanin gwamnati, yayin da waɗanda suka ƙi bi su za su fuskanci hukunci
  • Kalamansa sun janyo suka kan dimokuraɗiyya, ’yancin faɗar albarkacin baki da kuma yadda jami’an gwamnati ke mu’amala da masu adawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Kwamishinan Matasa da Bunƙasa Wasanni na Jihar Borno, Sainna Buba, ya janyo cece-kuce bayan ya yi barazanar ɗaukar mataki kan abokan hamayyar siyasa da masu adawa da jam’iyyar APC.

Buba ya yi kalaman ne a wajen ƙaddamar da wani kamfen da Tinubu City Boy Movement, ƙungiyar da ke goyon bayan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da yiwuwar sake tsayawa takararsa a zaɓen 2027, ta shirya.

Kara karanta wannan

Gwamna ya hana ayyukan 'Hisbah' a jiharsa, ya ba jami'an tsaro umarni

Sainna Buba ya yi wa masu adawa da APC barazana
Kwamishinan matasa da wasanni na Borno, Sainna Buba Hoto: Tijjani Mohammed Mohammed
Source: Facebook

“Za mu karya yatsunsa”

Da yake jawabi ga mahalarta taron, kwamishinan ya yi amfani da kalaman da ke ɗauke da barazana yayin da yake gargaɗin masu sukar gwamnati da ’yan adawa, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

“Wanda duk ya nuna mana yatsa, za mu nuna masa,” in ji Buba.

Ya ƙara da cewa:

“Yanzu siyasa muke yi. Duk wanda ya nuna mana yatsa, mu ma za mu nuna masa yatsa... Duk wanda ya sake nuna mana yatsa, za mu karya masa yatsansa.”

Kalaman sun janyo damuwa, musamman ganin cewa Buba jami’in gwamnati ne mai riƙe da mukamin kwamishina a jihar.

Ya yi magana kan amfana da gwamnati

Buba ya kuma yi kalaman da suka nuna cewa waɗanda suka goyi bayan jam’iyyar APC za su samu amfanin gwamnati, yayin da masu ƙin goyon bayan ta za su fuskanci hukunci.

“Gwamnati gwamnatin mu ce. A bi mu a sha zuma; wanda bai bi mu ba ya sha bulala." in ji shi

Kara karanta wannan

An gano abin da 'yan Najeriya za su yi da zai iya sa Tinubu faduwa a zaben 2027

Wannan magana ta ƙara janyo suka daga masu ganin cewa bai kamata a yi amfani da albarkatun gwamnati ko mukamin gwamnati wajen matsa wa jama’a su goyi bayan wata jam’iyyar siyasa ba.

An nuna damuwa kan dimokuraɗiyya

Masu sukar kalaman sun ce irin wannan furuci na iya yin illa ga tsarin siyasa mai gasa da kuma ’yancin ’yan ƙasa na zaɓar jam’iyyar da suke so.

Wasu daga cikin masu suka sun kuma bayyana cewa barazanar da jami’in gwamnati ya yi na iya haifar da fargaba a tsakanin masu adawa da gwamnati, tare da raunana haƙƙin faɗar albarkacin baki.

Yayin da shirye-shiryen zaɓen 2027 ke ƙara ɗaukar hankali, irin waɗannan kalamai na nuna yadda zafin siyasa ke ƙaruwa a wasu sassan ƙasar.

Buba da gwamnatin Borno ba su yi bayani ba

Ya zuwa lokacin wallafa rahoton, Buba bai fitar da wani bayani da ke fayyace ko kalamansa na barazana ne na zahiri ko kuma salon magana ne na siyasa mai tsauri ba.

Haka kuma, gwamnatin Jihar Borno ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan kalaman kwamishinan ba.

Lamarin ya faru ne kwanaki biyar bayan shugaban ƙaramar hukumar Kuje a Abuja, Danjuma Shekwolo, ya ce mazauna yankin su zaɓi APC a 2027 ko kuma su bar yankin.

Kara karanta wannan

Sanata Yari ya bayyana mutanen da za su taka muhimmiyar rawa a tazarcen Tinubu

Kwamishinan Borno ya yi barazana ga 'yan adawa
Taswirar jihar Borno, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

An bukaci a cafke shugaban karamar hukuma

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta bukaci hukumomin tsaro su gaggauta kama shugaban karamar hukumar Kuje da ke Abuja, Danjuma Shekwolo, bisa wasu kalamai da ya yi kan masu adawa da jam'iyyar APC.

ADC ta bayyana cewa kalaman Shekwolo na cewa mazauna Kuje su goyi bayan APC ko su bar yankin barazana ce ga hakkokin 'yan kasa da kuma wani yunkurin tilasta masu sauya matsayarsu ta siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng