Hotuna: Gwamnan Borno ya ziyarci mutanen da harin Boko Haram ya shafa a daren jiya

Hotuna: Gwamnan Borno ya ziyarci mutanen da harin Boko Haram ya shafa a daren jiya

Gwamnan jahar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya kai ziyarar jaje ga mutanen da mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram suka kai ma hari a daren Laraba, 12 ga watan Feburairu.

Yan ta’addan Boko Haram sun kai farmaki a unguwar Jiddari Polo dake garin Maidugurin jahar Borno jim kadan bayan ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai garin.

KU KARANTA: Yan siyasa ne suka biya ‘zauna gari banza’ don su yi ma Buhari ihu a Borno – Garba Shehu

Hotuna: Gwamnan Borno ya ziyarci mutanen da harin Boko Haram ya shafa a daren jiya
Zulum
Asali: Facebook

A wannan hari, yan ta’addan sun harba rokoki a kangidajen mutane, inda suka jikkata akalla mutane biyar, kuma sun kwashe tsawon mintuna talatin suna aman wuta a kan gidajen.

Wani mazaunin unguwar ya shaida ma jaridar TheCables a daren Laraba cewa: “A yanzu haka muna fuskantar barin wuta daga yan Boko Haram, yan ta’addan sun shigo ne bayan kimanin sa’o’i biyu da tafiyan shugaban kasa.”

A wani labarin kuma, hukumar majalisar dokokin Najeriya ta bayyana damuwarta game da yiwuwar kungiyar ta’adda ta kaddamar da harin ta’addanci a majalisa, kamar yadda wani babban jami’in hukumar ya bayyana.

Hotuna: Gwamnan Borno ya ziyarci mutanen da harin Boko Haram ya shafa a daren jiya
Zulum
Asali: Facebook

Wannan jami’I da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa: “Da gaske ne, mun samu mummunan rahoton tsaro dake bayyana cewa majalisar dokokin Najeriya na daga cikin wuraren da yan ta’adda ke shirin kaddamar da hari, kuma ba na wasa bane.”

Jami’in yace suna yawan samun bakin fuskoki dake shiga cikin majalisa a yan kwanakin nan, kuma hakan ya zama abin damuwa ga hukumar majalisar, kamar yadda ya shaida ma majiyar Legit.ng.

Jami’in ya kara da cewa a lokutta da dama da zarar jami’an hukumar ko jami’an tsaro sun tunkari wadannan bakin fuskoki game da dalilin zuwansu majalisar sai su ce sun zo wurin wakilansu ne, bugu da kari jami’an tsaron majalisar sun yi karanci.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel