Buhari ya dawo Najeriya, ya sauka a Maiduguri don yiwa gwamnan Borno ta’aziyya

Buhari ya dawo Najeriya, ya sauka a Maiduguri don yiwa gwamnan Borno ta’aziyya

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo gida Najeriya bayan ya halarci wani taro a kasar Habasha

- Daga Addis Ababa kai tsaye Buhari ya wuce Maiduguri domin yiwa gwamna da mutanen Borno jajen kisan wasu matafiya da yan ta'addan Boko Haram suka yi a kwanan nan

- Kakakin shugaban kasar Garba Shehu ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Laraba, 12 ga watan Fabrairu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo kasar bayan halartan taron AU na 33 a kasar Habasha.

Legit.ng ta rahoto cewa babban mai ba Shugaban kasa shawara kan kafofin watsa labarai, Garba Shehu ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Laraba, 12 ga watan Fabrairu.

Ya ce Shugaba Buhari, ya taso daga Addis Ababa sannan a yanzun nan ya sauka a Maiduguri, babbar birnin jahar Borno.

Shugaban kasar zai kai ziyarar jaje ne ga gwamnati da mutanen jahar Borno biyo bayan mummunan lamarin da ya afku kwanan nan inda yan ta’addan Boko Haram suka kashe matafiya da dama.

Hakazalika, hadimin shugaan kasar, Bahir Ahmad ya wallafa bidiyon ziyarar a shafinsa na Twitter.

KU KARANTA KUMA: Ta bayyana: Gaskiyar dalilin da yasa Kwankwaso da Abba gida-gida basu tarbi masoyinsu da ya yi tattaki daga Katsina ba

A wani labarin kuma, mun ji cewa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa rashin gaskiya ya ratsa jinin ‘Yan Najeriya, don haka ake samun matsala wajen yakin da ya dauko.

Jaridar Vanguard ta rahoto shugaban kasar ya na kukan tun kafin hawansa mulki a shekarar 2015, rashin gaskiya da yin ba daidai ba, ya bi cikin jikin mutane.

Muhammadu Buhari ya nuna cewa sabo da rashin gaskiya ne ya sa ba a ganin tasirin kokarin da ya ke yi a wasu wurare, duk da haka ya ce ba zai ja da baya ba.

A wajen kaddamar da wani littafi da tsohuwar shugabar EFCC, Farida Waziri ta rubuta, Buhari ya ce dole a tsaya tsayin daka wajen ganin an yaki rashin gaskiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel