Ziyarar Borno: Ku ba Buhari hakuri yanzun nan – Kungiya ga gwamnan APC da hadimansa

Ziyarar Borno: Ku ba Buhari hakuri yanzun nan – Kungiya ga gwamnan APC da hadimansa

- Wata kungiya ta yi kira ga gwamnan jahar Borno da hadimansa da su ba shugaba Buhari hakuri

- Kungiyar ta ce gwamnan ya yi yunkurin kunyata Shugaban kasa a yayin ziyarsa zuwa jahar Borno

- A cewar kungiyar, ba zai taba yiwuwa a ce wadannan mutanen Borno da suka fito kwansu da kwarkwatarsu don mara wa shugaba Buhari baya sun juya masa ba

Yan sa'o'i bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zargi shugabannin jahar Borno da gaza ba gwamnatinsa hadin kai wajen yaki da ta'addanci a yankin arewa maso gabas, wata kungiya ta yi zargin cewa gwamnan jahar da hadimansa ma na da tambayoyin amsawa kan haka.

A wani taron manema labarai a Abuja a ranar Alhamis, 13 ga watan Fabrairu, kungiyar Borno Coalition for Justice (BCJ) ta ce Babagana Zulum da hadimansa sun yi wani yunkuri na kunyata shugaban kasa Buhari.

Ziyarar Borno: Ku ba Buhari hakuri yanzun nan – Kungiya ga gwamnan APC da hadimansa
Ziyarar Borno: Ku ba Buhari hakuri yanzun nan – Kungiya ga gwamnan APC da hadimansa
Asali: Facebook

Kungiyar wacce ta bayyana lamarin da ya afku a lokacin ziyarar shugaban kasar a matsayin "makircin tozarta shugaba Buhari wanda hadiman gwamnan Borno suka shirya" cewa ta ce hakan ya nuna "tsoro da rashin hankali sannan kuma cewa tabbaci ne ga tsanar da gwamnan ya yi wa shugaban kasar".

Jagoran kungiyar, Mohammed Ali, ya ce shugaban kasar na da babban matsayi a jahar tun daga jajicewarsa a zamanin da ya ke a matsayin soja.

Ali ya ce ba zai yiwu a ce wadannan mutanen dai sun juya masa baya ba.

KU KARANTA KUMA: Namibia: Matar shugaban kasa za ta bayar da dukiyarta sadaka

Ya shawarci Zulum da ya kira hadimansa na siyasa sannan su je su ba shugaban kasa hakuri.

Sannan Ali ya roki shugaba Buhari da kada ya yi kasa a gwiwa sannan ya ci gaba da manufarsa kan rashin tsaro ta hanyar kaddamar da dokar ta baci a kan jahar.

A wani lamarin kuma, mun ji cewa Gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta dauki alkawarin biyan kudin fansan duk barnar da Boko Haram ta yi a garin Auno tare da sabunta dukkanin gidajen da suka lalata a garin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel