Jihar Borno
Ma'aikatan tallafi da ke taimakon 'yan gudun hijira a halin yanzu sun cikin wani hali bayan 'yan ta'adda sun kaddamar da hari a Dikwa. Mayakan ISWAP ne suka je.
A wani sabon bidiyo da kungiyar Jihadi ta Boko Haram ta fitar, an ga yara kanana ana koyar da su addini da kuma horar da su fada a sansaninsu, HumAngle tace.
Ma'aikatan gyaran wutan lantarki a yankin jihar Borno sun ci karo da nakiyar da ta fashe dasu da motar da suke ciki. Ma'aikatan na kan hanyarsu ne ta zuwa gyara
Mayakan Boko Haram sun saki amaryar da suka sace ranar Alhamis a kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu a yayinda ake mata rakiya zuwa dakin mijinta na aure.
Sojojin Najeriya sun datse farmakin da 'yan kungiyar ta'addanci ta ISWAP da Boko Haram suka kaiwa fasinjoji a kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu a Auno.
Kwamandan Boko Haram Abubakar Shekau ya yi ikirarin cewa shi ya dauka nauyin tashin bama-bamai a Maiduguri a ranar Talata. Ya ce yana farin ciki da nasararsu.
Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya bayyana cewa jiharsa na da shirin daukar nauyin samar da filin kiwo ga makiyaya da yakai girman hekta 5,000 a dajin jihar.
Dakarun sojin Najeriya sun samu nasarar kwato garin Marte daga hannun miyagun 'yan ta'addan Boko Haram, kakain rundunar sojin kasa ya tabbatar da wannan cigaba.
Rahotanni sun nuna cewa dakarun sojin kasar Najeriya sun tarwatsa wasu nakiyoyi da Boko Haram suka saka a hanya mai zuwa Marte ta jihar Borno a matsayin tarko.
Jihar Borno
Samu kari