Zulum: Ba zamu kori makiyaya ba, zamu samar da filin kiwo hekta 5,000 garesu

Zulum: Ba zamu kori makiyaya ba, zamu samar da filin kiwo hekta 5,000 garesu

- A kokarin inganta harkar kiwo a yankin, ya alkawarta samar da fili hekta 5,000 a jihar

- Gwamnan ya bayyana ra'ayinsa na tallafawa makiyaya a jiharsa ba wai fatattakarsu ba

- Ya kuma kirayi sauran jihohin arewa da su duba lamarin samar da wuraren kiwo a jihohinsu

Gwamnatin jihar Borno ta ce za ta samar da wuraren kiwo ga makiyaya wadanda ke son kafa kasuwanci a jihar, The Punch ta ruwaito.

Gwamnan jihar, Farfesa Babagana Zulum, ya ce jihar Borno na da filin noma mai fadin kusan kilomita murabba'in dubu 73 wanda zai iya daukar yawan makiyaya.

Gwamnan ya yi wannan bayanin ne a ranar Litinin a yayin kaddamar da fara aikin gaggawa na Hukumar Kula da Yankin Arewa-maso-Gabas a Maiduguri.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: Gwamnan jihar Oyo ya bada umarnin sake bude kasuwar Sasha a yau

Zulum: Ba zamu kori makiyaya ba zamu samar da filin kiwo hekta 5,000 garesu
Zulum: Ba zamu kori makiyaya ba zamu samar da filin kiwo hekta 5,000 garesu Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Zulum ya bayyana cewa, ya kasance yana goyon bayan samar da wuraren kiwon makiyaya a tsakanin jihohi shida na Arewa maso Gabas domin hakan ba zai samar da ci gaban tattalin arziki ga yankin ba kawai, zai bunkasa har da jerin kayan amfanin gona na yankin. .

Ya ce, “Muna da filayen noma a nan Arewa maso Gabas. Na dade ina ba da fatawar a kirkiro da wuraren kiwo a jihar. Kowace jiha a Arewa-maso-Gabas na iya samar da akalla hekta 5,000 na cibiyoyin kiwo inda za mu bunkasa kiwon dabbobi har miliyan biyu zuwa uku."

Gwamnan ya ce yayin da wasu ke korar makiyaya daga jihohin su da yankin su, jihar Borno za ta nemi samar da filaye don kafa cibiyoyin da za su taimaka wajen samar da dabbobi da kuma bunkasa ayyukan noma a jihar.

KU KARANTA: Elon Musk ya rasa N5trn dalilin Bitcon ya sauka daga matsayin wanda ya fi kowa kudi a duniya

A wani labarin, Yayin da ‘yan Najeriya ke fama da kalubalen tattalin arziki, yanzu kuma dillalan shanu na barazanar shiga yajin aiki a fadin kasar.

Hadaddiyar kungiyar dillalan abinci da shanu ta Najeriya (AFUCDN) ta nuna rashin jin dadin ta da cewa ana kashe mambobinta a sassa daban-daban na kasar.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel