'Yan Adawa za Su Yi Babban Taro a Yau domin Shirin Kifar da Tinubu a 2027
- Jam’iyyun adawa a Najeriya za su gudanar da wani babban taro a Abuja domin tattauna yadda za su haɗa ƙarfi tare da samar da dabarun kayar da Bola Ahmed Tinubu
- Jam’iyyar SDP da PRP sun tabbatar da halartar taron, yayin da PDP ta ce ba ta da masaniya kan taron kuma ba za ta shiga duk wata tattaunawar hadaka ba
- Ƙungiyar G-100 ce ta shirya taron, inda ake sa ran shugabannin jam’iyyun adawa da masu ruwa da tsaki a siyasa za su tattauna hanyoyin haɗin gwiwa gabaninzaɓen 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Jam’iyyun adawa a Najeriya sun shirya taruwa a Abuja a yau Litinin domin tattauna yiwuwar haɗa ƙarfi da kuma samar da wata hanya ta kayar da Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC a zaɓen 2027.
Taron wanda ƙungiyar matsin lamba ta siyasa G-100 ta shirya, na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun saɓani tsakanin jam’iyyun adawa kan batun haɗin gwiwa da kuma wanda zai zama ɗan takarar da za su marawa baya.

Source: Facebook
Punch ta rahoto cewa jam’iyyar SDP da PRP sun tabbatar da cewa za su halarci taron, yayin da PDP ta bayyana cewa ba ta da masaniya game da shi.
Manufar taron 'yan G-100
Ƙungiyar G-100, wadda tsohon Darakta-Janar na PGF, Salihu Lukman, ke jagoranta, ta ce adawar da ta rabu gida-gida za ta sha wahala wajen kayar da jam’iyyar da ke mulki saboda irin ƙarfin tsari da kuɗaɗen da take da su.
A wata sanarwa da Lukman ya sanya wa hannu ranar Lahadi, ƙungiyar ta bukaci jam’iyyun adawa su ajiye bambance-bambancensu gefe guda tare da halartar taron cikin shirin yin haɗin gwiwa.
Ta ce taron ya zo ne a wani muhimmin lokaci ga dimokuraɗiyyar Najeriya, inda miliyoyin ’yan ƙasa ke kallon adawa ba kawai domin su soki gwamnati ba, sai dai su nuna ƙwarewa da kishin ƙasa wajen samar da sauyi.

Source: Facebook
Batun kuri’un 'yan adawa
G-100 ta kuma ce za a tattauna hanyoyin da jam’iyyun adawa za su iya haɗa kai wajen sa ido kan zaɓe da kuma kare kuri’unsu.
Ta ce zaɓukan baya sun nuna cewa rarrabuwar kawuna tsakanin jam’iyyun adawa kan iya ƙara wa jam’iyyar da ke mulki damar ci gaba da kasancewa a kan mulki.
ADC ta ce za ta yi nasara
A wani labarin, mun ruwaito cewa jam’iyyar ADC ta ce ba ta bukatar haɗin gwiwar jam’iyyun adawa domin kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Kakakin jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya ce ɗan takararta na shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, na da ƙarfin da zai iya cin zaɓen ba tare da wata babbar ƙawance ta adawa ba.
Ya bayyana cewa duk da cewa jam’iyyar ta yi imanin tun farko cewa haɗa kan jam’iyyun adawa zai sauƙaƙa kayar da APC, abubuwan da suka faru daga baya sun sauya wannan tunanin.
Asali: Legit.ng

