Da duminsa: Sojoji sun mamaye Dikwa, sun fatattaki mayakan Boko Haram

Da duminsa: Sojoji sun mamaye Dikwa, sun fatattaki mayakan Boko Haram

- Zakakuran dakarun sojin Najeriya sun mamaye garin Dikwa bayan 'yan ta'adda sun yi yunkurin kwacewa

- 'Yan ta'addan ISWAP da na Boko Haram sun kai farmaki garin bayan da Gwamna Zulum ya kai tallafin kayan abinci

- Rashin samun wannan damar ne yasa 'yan ta'addan suka dasa bama-bamai a kan hanyar shiga garin

Rundunar sojin Operation Lafiya Dole ta fattaki 'yan ta'addan Boko Haram da na ISWAP wadanda suka yi yunkurin kaiwa garin Dikwa hari tare da kwacta a jihar Borno.

Kungiyoyin ta;addancin sun tsinkayi garin da yawansu a motocin yaki da babura amma sun ci karo da ruwan wuta tare da karfin zakakuran bataliya ta 81 da ta samu taimakon sojin saman rundunar Operation Lafiya Dole.

'Yan ta'addan sun yi yunkurin ratsa garin inda suka yi kokarin kwashe kayan abinci bayan labarin raba kayan abincin da Farfesa Babagana Zulum yayi ya riskesu.

KU KARANTA: Da duminsa: Mayakan ISWAP da sojin Najeriya ana musayar wuta a Dikwa, Borno

Da duminsa: Sojoji sun mamaye Dikwa, sun kwace garin daga hannun Boko Haram
Da duminsa: Sojoji sun mamaye Dikwa, sun kwace garin daga hannun Boko Haram. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

Sun taho ta bangaren garin Marte amma sun kasa shiga saboda dakarun sojin da ke cikin garin kuma a shirye suke ko da za ta cabe.

'Yan ta'addan sun rasa yadda za su yi saboda nasarar da dakarun suka samu na kwace garin Marte.

A cike da fushi tare da rasa yadda za su yi suka dasa bama-bamai a hanyar wanda babu kakkautawa zakakuran dakarun sojin Najeriya suke cire su.

Kamar yadda kakakin rundunar sojin kasa, Birgediya Janar Mohammed Yerima ya sanar a takardar da ya fitar, Manjo Janar Attahiru na jinjinawa kokarin sojin Najerya ta yadda suka shawo kan lamarin.

KU KARANTA: Sule Lamido: Salihu Yakasai ya fi Adesina da Garba Shehu jarumta

A wani labari na daban, babban malamin addinin Islama kuma tsohon babban alkalin yankin arewa, Ahmad Gumi ya kwatanta garkuwa da yaran makaranta da 'yan bindiga ke yi da karamin laifi.

Gumi ya ce garkuwa da yaran makaranta da 'yan bindiga ke yi ba babban laifi bane idan aka hada shi shiga kauyuka tare da kashe jama'a da suke yi.

Gumi ya sanar da hakan ne yayin tattaunawa da bangaren Pidgin na BBC.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: