Satar fasinjoji: Sojoji sun dakile Boko Haram a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri

Satar fasinjoji: Sojoji sun dakile Boko Haram a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri

- Dakarun sojin Najeriya sun dakile farmakin da 'yan ISWAP da Boko Haram suka kaiwa fasinjoji

- 'Yan ta'addan sun tunkari fasinjojin a babbar hanyar Maiduguri zuwa Auno dauke da miyagun makamai

- Tuni dakarun bataliya ta 212 da ke Jakana, Goni Masari da Auno suka isa wurin tare da fattattakar 'yan ta'addan

Sojojin Najeriya sun datse farmakin da 'yan kungiyar ta'addanci ta ISWAP da Boko Haram suka kaiwa fasinjoji a kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu a Auno da ke jihar Borno.

Duk da sojin sun fatattaki 'yan ta'addan, majiyar sirri daga rundunar ta sanar da PRNigeria cewa an ceto fasinjoji masu tarin yawa da ke ababen hawa na haya a Auno.

Dakarun bataliya ta 212 da ke Jakana, Goni Masari da Auno sun gaggauta zuwa wurin sannan suka raka fasinjojin zuwa Damaturu da Maiduguri.

KU KARANTA: 'Yan bindiga daga saman bishiya sun sheke dan sanda, sun raunata wasu 3 a Neja

Satar fasinjoji: Sojoji sun dakile Boko Haram a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri
Satar fasinjoji: Sojoji sun dakile Boko Haram a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri. Hoto daga @BBCHausa
Source: Twitter

Majiyar tace: "'Yan ta'addan sun isa da yawansu sanye da bakaken kaya a motocin yaki. Sun kara da wasu miyagun makamai. Wasu sun fente fuskarsu da gawayi.

"Sun je yankin da niyyar sace fasinjoji masu yawa sannan su kaiwa dakarun soji farmaki."

Wata majiya a wurin da abun ya auku ta ce: "Lamarin ya shafa wasu motoci biyu kirar gulf cike da fasinjoji, babbar mota da wata bus ta Borno Express.

"Amma kuma an bankawa motar kirar gulf guda daya inda fasinjoji suka tsere. Yayin da wasu sojojin suka fatattaki 'yan ta'addan, sauran sun tsare babbar hanyar tare da raka fasinjojin."

KU KARANTA: Majalisar dattawa ta fadi dalilinta na tabbatar da Bawa a matsayin shugaban EFCC

A wani labari na daban, kwamandan Boko Haram Abubakar Shekau ya yi ikirarin cewa shi ya dauka nauyin tashin bama-bamai a Maiduguri a ranar Talata.

A kalla mutane 10 ne suka rasa rayukansu a yayin harin da 'yan ta'adda suka kai, ganau suka tabbatar. Wasu mutane 50 sun samu miyagun raunika kamar yadda gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya sanar.

"Ina matukar farin ciki da wannan nasarar da mayakanmu suka samu," Shekau ya sanar a wani bidiyo da Channels TV ta gani.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Source: Legit.ng

Online view pixel