An Lissafa Biliyoyin da Tinubu da Remi Suka Kashe a Tafiye Tafiyen shekaru 3

An Lissafa Biliyoyin da Tinubu da Remi Suka Kashe a Tafiye Tafiyen shekaru 3

  • Shugaba Bola Tinubu ya kwashe kwanaki 261 a wajen Najeriya cikin balaguro 51 da ya yi zuwa ƙasashe daban-daban
  • Babu inda shugaban kasar ya fi zuwa irin Faransa, sannan ya yi tafiye-tafiye da da-dama zuwa Saudi da Birtaniya
  • An fitar da dalar Amurka $553,884 (daidai da N700.7m) domin yawon da Matar shugaban kasa, Oluremi Tinubu ta yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Fadar shugaban kasar Najeriya ta ci biliyoyin kudi wajen tafiye-tafiyen cikin gida da kuma zuwa kasashe na ketare.

A cikin shekaru uku da ‘yan watanni da Bola Ahmed Tinubu ya yi a kan mulki, tafiye-tafiye sun ci wa gwamnati sama da N37.64bn.

Bola Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu lokacin wani balaguro Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tafiye-tafiyen Shugaban Najeriya a shekaru 3

Wadannan bayanai sun fito ne daga GovSpend, wata kafa ta musamman da aka tanada domin bibiyen kashe-kashen kudi a Najeriya.

Kara karanta wannan

Shugabannin kwamitin yakin zabe da aka yi kafin Abdulaziz Yari daga 1999 zuwa 2027

Daga Yunin 2023 zuwa watan Afrilun shekarar nan ta 2026, Bola Ahmed Tinubu da matarsa suka kashe sama da N30bn wajen balaguro.

Daily Trust ta bi diddigi ta gano cewa daga shigansa ofis zuwa yau, shugaba Tinubu ya shafe kwanaki akalla 261 a wajen Najeriya.

Daga 2023 zuwa yau kuma, ya yi tafiya sau 52 kenan idan aka hada da hutun da ya tafi yanzu, inda zai shafe makonni uku a nahiyar Turai.

Binciken da aka yi ya nuna N37,639,227,853.51 sun tafiya wajen yawon hutu, tafiye-tafiye, dawainiya, canjin kudi da makamantansu.

A shekarar 2023 da ya hau mulki, ya kashe N9,185,966,339.75. Watanni 24 na 2024 da 2025 sun ci N25,269,969,240.92 da N2,705,843,328.38.

Tafiye-tafiyen da aka yi a watanni hudun farko na 2026 sun ci N477,448,944.46. abin da aka kashe a 2025 ya fi na kowace shekara yawa.

Cikin tafiye-tafiye 51 da ya yi zuwa ketare, Tinubu ya ziyarci kasashe akalla 30. Kuma babu inda ya fi zuwa irin Faransa sai Saudi da Ingila.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Atiku ya gano shaidar da ke nuna asalin shekarun Bola Tinubu a duniya

Matar shugaban kasa ta ci N700m a tafiya

An ji cewa yawon da Mai dakin shugaban kasa ta yi sun jawo an kashe N700m a shekara guda.

Sai da gwamnati ta batar da $553, 000 a dalilin kasashe irinsu Mozambique, Ethiopia, Ingila da Faransa da ta ziyarta a 2023 da 2024.

Kasashen da Tinubu ya je tun daga 2023

Daga shigansa ofis a Yunin shekarar 2023 ya ziyarci Faransa. Bayan nan ya je kasashen Guinea-Bissau da Kenya a nahiyar Afrika.

Bayan nan ya ziyarci Indiya, UAE, Amurka, Jamus, Saudi kuma ya sake zuwa Guinea-Bissau da Faransa, UAE da Saudi Arabiya.

Ana shiga 2024 ya tafi hutu a Faransa kafin ya wuce Ethiopia. A lokacin ya je Qatar, Sanagal, Netherlands, Saudi, Ingila da kasar Chadi.

Idan za a tuna a lokacin ya kuma zuwa Faransa ban da tafiyarsa zuwa China da Ingila.

Tinubu
Bola Tinubu lokacin da ya je kasar waje da Shugaban Najeriyan a Aso Rock Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ghana, UAE, Tanzaniya, Faransa, Ethiopia da Ingila su ne kasashen da Tinubu ya fara zuwa a 2025. Daga baya kuma ya ziyarci Vatican.

Kara karanta wannan

Yadda batun maido tallafin mai ya zafafa adawa tsakanin Tinubu da Atiku

A shekarar aka ga shugaban Najeriya a Saint Lucia kuma ya je Brazil, Japan, Ingila da Faransa har sau biyu - inda ya saba zuwa hutu.

Wannan shekara kuwa an gan shi a kasashen UAE, Turkiyya, Ingila, Kenya, Faransa, Ruwnda daga Junairu zuwa tsakiyar watan Mayu.

Atiku ya zargi gwamnatin Tinubu da karya

Ana da labari cewa ganin kamar lissafi bai fita ba game da rabon N600bn da aka yi a gidaje ya sa Atiku Abubakar ya sake tabo gwamnati.

'Dan takaran ADC a 207 ya soki gwamnatin Bola Tinubu a kan zancen rarraba ₦600bn ga talakawa, ya ce akwai baki biyu a maganar da ta yi.

Atiku Abubakar ya nemi jin meyasa da farko gwamnati ta ce ta taimaki mutane miliyan 15, daga baya sai aka rage adadin zuwa miliyan 10.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng