Shekau ya magantu a kan tashin bama-bamai a Maiduguri da kwace gonarsa

Shekau ya magantu a kan tashin bama-bamai a Maiduguri da kwace gonarsa

- Shugaban 'yan ta'addan Boko Haram, Abubakar Shekau ya ce su ke da alhakin tashin bama-bamai a Maiduguri

- A cewarsa, koda mutum yana sallah tare da zakka matukar yana bin al'adun Turawan yamma ba Musulmi bane

- Shekau ya kara da musanta cewa sojin Najeriya sun kwace gonarsa, ya ce ya kafa daular Musulunci

Kwamandan Boko Haram Abubakar Shekau ya yi ikirarin cewa shi ya dauka nauyin tashin bama-bamai a Maiduguri a ranar Talata.

A kalla mutane 10 ne suka rasa rayukansu a yayin harin da 'yan ta'adda suka kai, ganau suka tabbatar.

Wasu mutane 50 sun samu miyagun raunika kamar yadda gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya sanar.

"Ina matukar farin ciki da wannan nasarar da mayakanmu suka samu," Shekau ya sanar a wani bidiyo da Channels TV ta gani.

KU KARANTA: Damfara: Maina ya fadi babu nauyi, kotu ta soke bukatar belinsa

Da duminsa: Shekau ya dauka alhakin tashin bama-baman Maiduguri
Da duminsa: Shekau ya dauka alhakin tashin bama-baman Maiduguri. Hoto daga @Channelstv
Source: Twitter

Ya kara da musanta cewa sojojin Najeriya sun kwace gonarsa inda yayi tunkaho da cewa yayi nasarar kafa daular Musulunci.

"Kada ka kira kanka Musulmi saboda kana sallah kuma kana bada zakka. In har ka rungumi al'adun turawan yamma baka cikinmu. Ba za mu taba zama wuri daya ba har sai ka mika wuya ga Allah," yace.

KU KARANTA: Ka zo mu tattauna, baka son kawo zaman lafiya, 'Yan bindiga sun gayyaci Buhari

A wani labari na daban, majalisar dattawa ta kare kanta a kan hukuncin da ta yanke na tabbatar da sabon shugaban hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, Abdulrasheed Bawa.

Tabbatar da Bawa a matsayin shugaban hukumar EFCC ya faru ne a ranar Laraba jim kadan bayan ya bayyana gaban majalisar dattawan kuma sun tantancesa.

Tabbatar da Bawa tazo ne a lokacin da ake ta zargi tare da cece-kuce a kan rahoton cewa an taba kama sabon shugaban EFCC da laifin rashawa, Channels TV ta ruwaito.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Source: Legit.ng

Online view pixel