Yanzun nan: Yan ta’addan Boko Haram sun saki amaryar da aka sace a Borno

Yanzun nan: Yan ta’addan Boko Haram sun saki amaryar da aka sace a Borno

- Mayakan Boko Haram sun saki wata amarya da suka yi garkuwa da ita a hanyar Maiduguri zuwa Damaturu

- Amaryar ta fada tarkon garkuwar mayakan ne tare da wasu kawayenta da 'yan uwa yayin da suke rakiyarta dakin miji

- Sai dai babu tabbacin ko an biya kudin fansa kafin sakin nasu

An saki amaryar da aka sace a babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu a ranar Alhamis.

An sace ta tare da kawayenta da kuma wasu mutane da ke bin hanyar a lokacin da maharan suka kai harin.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa maharan sun sauke wadanda lamarin ya rutsa da su a wani kauye kusa da Damaturu, babban birnin jihar Yobe, da tsakar dare.

KU KARANTA KUMA: Tanko Yakasai ya tabbatar da cewar jami’an tsaro sun kama dansa hadimin Ganduje

Yanzun nan: Yan ta’addan Boko Haram sun saki amaryar da aka sace a Borno
Yanzun nan: Yan ta’addan Boko Haram sun saki amaryar da aka sace a Borno Hoto: Premium Times
Source: UGC

Babu tabbacin ko an biya kudin fansa.

Babagana Kashim, daya daga cikin dangin wacce lamarin ya rutsa da ita, ya tabbatar da cewa a halin yanzu amaryar da kawayenta suna kwance a wani asibiti da ba a bayyana ba a Damaturu.

“Tabbatacce ne cewa an sake su. Maharan sun sauke su ne a wani kauye da ke kusa da Damaturu.

“A yanzu da muke magana, suna samun kulawar likita a wani asibiti da ba a bayyana ba a Damaturu. Muna farin ciki daga karshe sun dawo gida," inji Babagana.

An gudanar da bikin cikin nasara a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, amma an yi garkuwa da mutanen a hanyarsu ta zuwa Damaturu.

A baya mun kawo cewa ‘yan ta’addan da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne, sun kai hari a kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri.

Rahotanni daga jaridar Yerwa Express sun bayyana cewa ‘yan ta’addan sun tare babban titin na jihar Borno, sun yi gaba da wasu matafiya da su ka samu.

KU KARANTA KUMA: Ta tabbata: Ba sauran kaiwa kudu kayan abinci, tirelolin Albasa sun bar Nigeria

Majiyar ta ce dakarun sojojin Najeriya sun samu labarin wannan hari, kuma sun yi maza sun maida martani, su na shirin ceto fasinjoji da aka yi gaba da su.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Source: Legit.ng

Online view pixel