Da duminsa: Sojojin Najeriya sun kwato garin Marte daga hannun Boko Haram
- Zakakuran dakarun sojin kasa na Najeriya sun kwato garin Marte da kewaye daga hannun 'yan ta'adda
- Kamar yadda Mohammed Yerima, kakakin rundunar sojin kasan ya tabbatar, ya ce sun kwace yankin
- A ranar Lahadi ne Manjo Janar Attahiru ya bada wa'adin sa'o'i 48 na kwace yankin daga hannun mayakan ta'addanci
Dakarun sojin Najeriya sun samu nasarar kwato garin Marte daga hannun miyagun 'yan ta'addan Boko Haram, kakakin rundunar sojin kasa ya tabbatar da wannan cigaban.
Rundunar ta samu wannan nasarar ne a ranar Talata bayan umarnin da shugaban rundunar sojin kasa, Manjo Janar Attahiru ya basu tare da wa'adi.
KU KARANTA: Ka yi murabus idan ba za ka iya shawo kan matsalar tsaro ba, CSO 43 ga Buhari
Mohammed Yerima, kakakin rundunar ya tabbatar da wannan cigaban ga jaridar The Cable a ranar Talata.
"Tabbas, mun sake kwace yankin," yace.
Wannan cigaban ya zo ne bayan da Ibrahim Attahiru, shugaban dakarun ya basu wa'adin sa'o'i 48 na kwato garin da kewaye daga hannun 'yan ta'adda.
Ya kara tabbatarwa da sojojin cewa za a samar da dukkan abubuwan da suke bukata domin su yi aiki mai gamsarwa.
Legit.ng ta ruwaito cewa, rahotanni sun nuna cewa dakarun sojin kasar Najeriya sun tarwatsa wasu nakiyoyi da Boko Haram suka saka a hanya mai zuwa Marte ta jihar Borno a matsayin tarkon halaka sojoji.
Hakan yana zuwa ne kasa da sa'o'i 48 bayan babban hafsan sojan kasa, Manjo Janar Ibrahim Attahiru ya bai wa dakarun wa'adain kwato Marte daga hannun mayakan ta'addancin.
Kamar yadda jaridar PRNigeria ta bayyana, banda manyan nakiyoyin da Boko Haram suka saka, 'yan ta'addan sun saje da farar hula a Marte don hana soji kai musu harin bama-bamai ta jiragen yaki.
KU KARANTA: Kyawawan hotunan zukekiyar 'yar gwamnan Bauchi yayin da ta zama cikakkiyar likita
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng