Abubakar Shekau zai kamu da addu'a, in ji Fasto Elijah Ayodele

Abubakar Shekau zai kamu da addu'a, in ji Fasto Elijah Ayodele

- Primate Elijah Ayodele mai cocin INRI Evangelical Spiritual Church ya ce ana iya kama Shekau ta addu'o'i

- Malamin addinin kiristan, ya ce shugaban na Boko Haram ba aljani bane don haka idan zai kamu da addu'o'i

- Primate Elijah Ayodele ya kuma ce fastocin Nigeria sun san inda Shekau ya ce amma gwamnati ba ta sauraronsu

Wanda ya kafa cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele ya ce ana iya kama shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau ta hanyar yin addu'o'i, PM News ta ruwaito.

Primate Ayodele cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin ya ce shugaban na kungiyar 'yan ta'addar ta Boko Haram ba aljani bane don haka za a iya kama shi ta hanyar yin addu'o'i.

Abubakar Shekau zai kamu da addu'a, in ji Fasto Elijah Ayodele
Abubakar Shekau zai kamu da addu'a, in ji Fasto Elijah Ayodele. Hoto: @PMNews
Source: Twitter

A cewarsa, fastoci da manzoni a kasar nan sun san inda Shekau ya ke boye wa.

DUBA WANNAN: Yanzun nan: 'Yan Boko Haram sun ƙwace Dikwa da dubban mutane cikin garin

Ya kuma ce shi da sauran fastoci za su iya tona wadanda ke daukan nauyin yan bindiga, garkuwa da sauran laifuka da ake tafkawa a kasar.

Malamin addinin ya koka kan yadda gwamnatin Nigeria bata da tsoron Allah, wanda hakan ya haifar da barazana ga rayyuka da dukiyoyin yan kasar.

Ayodele, cikin sanarwar da ya rabawa manema labarai ya kuma yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari ya koma gefe ya bari a gudanar da wani zabe a shekarar 2023.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun yi barazanar kashe mu, su soya namar mu su cinye, Ɗalibar Jangebe

"Ana barazana ga ilimi, kuma Shekau ba aljani bane, za a iya kama shi da addu'o'i amma gwamnati bata tsoron Allah.

"Fastoci, annabawa za su iya fada musu inda Shekau ya ke da wadanda ke daukan nauyin laifuka a Nigeria amma ba za su saurara ba. Mene gwamnatin nan ta yi tun 2019?

"Za su iya nuna mana abinda suka cimma a bangaren tsaro, ilimi, gine-gine? Buhari ya koma gefe ya bari a yi wani zabe a 2023," in ji shi.

A wani labarin daban, kun ji Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi, NDLEA, ta kama wani mai fataucin miyagun kwayoyi mai shekaru 36 dauke da hodar Iblis da ta kai na Naira biliyan daya.

NDLEA ta ce mai safarar, Nkem Timothy, wanda ya yi basaja a matsayin Auwalu Audu domin yin fataucin kunshin hodar Iblis da nauyinsa ya kai 1.550kg. An yi kiyashin kudinsa ya kai Naira biliyan 1.

Kakakin NDLEA, Femi Babafemi ya ce an kama wanda ake zargin ne yayin da ya ke kokarin zuwa Algeria ta bodar jamhuriyar Nijar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Source: Legit.ng

Online view pixel