Yanzu Yanzu: Boko Haram ta saki wani fasto da ta sace bayan watanni 2

Yanzu Yanzu: Boko Haram ta saki wani fasto da ta sace bayan watanni 2

- Mayakan Boko Haram sun saki Bulus Yikura, wani faston Najeriya bayan ya kwashe watanni a hannun su

- An sace malamin ne a watan Disambar shekarar 2020 lokacin da wasu mahara suka kai hari jihar Borno

- Wadanda aka saki, a cewar majiyoyin tsaro sune ma’aikatan kungiyar agaji ta Red Cross, IOM da sauran kungiyoyi masu zaman kansu na kasa da kasa

An saki Bulus Yikura, wani faston Najeriya da ke cocin EYN wanda maharan Boko Haram suka sace, kamar yadda jaridar Premium Times ta fitar, tana mai tabbatar da hakan daga majiyoyin tsaro.

A cewar rahoton, Yikura ya samu ‘yanci ne a yammacin ranar Laraba, 3 ga Maris, bayan kungiyar ta barshi ya tafi.

KU KARANTA KUMA: Tsohon dan takarar shugaban kasa, Shittu, ya koma jam'iyyar APC

Yanzu Yanzu: Boko Haram ta saki wani fasto da ta sace bayan watanni 2
Yanzu Yanzu: Boko Haram ta saki wani fasto da ta sace bayan watanni 2 Hoto: Kola Sulaimon
Source: Getty Images

An ganshi da misalin karfe 6:15 na yamma a cikin garin Maiduguri yayin da aka isar dashi ofishin Ofishin Tsaro na jihar Borno.

An sace Yikura ne a ranar 24 ga Disamba, 2020, lokacin da ‘yan ta’addan Boko Haram suka kai hari a kauyen Pemi da ke cikin karamar hukumar Chibok na jihar Borno.

Sakin nasa na zuwa ne bayan masu tayar da kayar bayan sun yada bidiyo inda Yikura ya roki gwamnatin tarayya da kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) da su cece shi kafin a kashe shi.

Masu garkuwan sun yi barazanar kashe shi a karshen wa’adin kwanaki bakwai da zai kare a ranar Alhamis, 4 ga watan Maris.

KU KARANTA KUMA: Dan adaidaita sahu ya mayar da N2.8m ga fasinja bayan ya tsinci kudin a cikin adaidaitarsa

A wani labarin, Kungiyar Kiristocin Najeriya ta nuna damuwarta cewa shirun da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi na tsawon lokaci game da wasu maganganun kwanan nan da shahararren malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi ya yi, yana nufin amincewa da ikirarin nasa.

Daya daga cikin irin wadannan ikirarin na Gumi shi ne cewa sojoji kirista su ne ke kashe barayi da masu tayar da kayar baya a kasar.

Kungiyar kiristocin ta yi kira ga Gumi da ya janye "kalaman rashin kishin kasa da rarrabuwa" da aka alakanta da shi domin neman zaman lafiya da hadin kan kasar.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Source: Legit.ng

Online view pixel