Hotuna: Boko Haram na horar da kananan yara a sabon bidiyon da ta fitar

Hotuna: Boko Haram na horar da kananan yara a sabon bidiyon da ta fitar

- Kungiyar Jihadi ta Boko Haram ta fitar da sabon bidiyo inda take horar da kananan yara

- A bidiyon mai tsayin mintina 16 da dakika 40, an ga kananan yara na koyon harbi da fada

- A wani bangare kuma, an ga yaran ana koyar da su addini tare da akidar Boko Haram

A wani sabon bidiyo da kungiyar Jihadi ta Boko Haram ta fitar, an ga yara kanana ana koyar da su addini da kuma horar da su fada a sansaninsu.

Hotunan sun nuna kananan yara sanye da kayan fada tare da marufin fuska inda ake koyar da su dambe, rike makamai da kuma koyar da su addini.

A kalla masu bada umarni biyu ne da yaro daya suka yi kama da Zastava M21, akwai yuwuwar daga jami'an tsaron kasar Kamaru suke.

Hotuna: Boko Haram na horar da kananan yara a sabon bidiyon da ta fitar
Hotuna: Boko Haram na horar da kananan yara a sabon bidiyon da ta fitar. Hoto daga @HumAngle
Source: Twitter

An ga wasu daga cikin yaran rike da wani irin katako da aka yi masa irin kirar wata bindiga mai suna Kalashnikov.

KU KARANTA: Satar 'yan makaranta: Hadimin Ganduje yace Buhari ya kawo karshen ta'addanci ko yayi murabus

Hotuna: Boko Haram na horar da kananan yara a sabon bidiyon da ta fitar
Hotuna: Boko Haram na horar da kananan yara a sabon bidiyon da ta fitar. Hoto daga @HumAngle
Source: Twitter

A wani sashi na bidiyon mai tsayin mintina 16 da dakika 40 wanda aka yi a harshen Hausa da Larabci, an ga wasu yaran ana koyar da su karatun addini da na akidar Boko Haram.

HumAngle ta ruwaito cewa a lokuta mabanbanta Boko Haram na nuna yara kanana da take horarwa domin cigaba da ta'addanci ko a nan gaba.

'Yan ta'addan Boko Haram da na ISWAP suna ta zubda jini a yankin arewa maso gabas na Najeriya da kuma tafkin Chadi wanda ya kai ga mutuwar a kalla mutum 30,000 kuma miliyan biyu suka rasa gidajensu.

Hotuna: Boko Haram na horar da kananan yara a sabon bidiyon da ta fitar
Hotuna: Boko Haram na horar da kananan yara a sabon bidiyon da ta fitar. Hoto daga @HumAngle
Source: Twitter

KU KARANTA: Iyayen yara sun ragargaza makarantar da aka sace dalibai mata a Zamfara, Malami

A wani labari na daban, a ranar Alhamis, 25 ga watan Fabrairun 2021, 'yan bindiga sun kai samame inda suka kashe a kalla mtum 22, Daily Trust ta wallafa.

Kamar yadda aka gani, lamarin ya faru a wani wurin hakar zinari da ke kusa da Sabuwar Tunga a kauyen Dankurmi da ke karamar hukumar Maru.

Kamar yadda wasu mazauna yankin suka sanar, 'yan bindigan sun kutsa wani kauyen na kusa mai suna Koda da niyyar satar shanu amma sai mazauna yankin suka bude musu wuta.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Source: Legit.ng

Online view pixel