Nasara daga Allah: Sojin Najeriya sun tarwatsa nakiyoyin da Boko Haram suka sa a Marte

Nasara daga Allah: Sojin Najeriya sun tarwatsa nakiyoyin da Boko Haram suka sa a Marte

- Rahotanni masu dadi na zuwa daga Borno inda sojin Najeriya suka hake nakiyoyin Boko Haram a Marte

- An gano cewa mayakan Boko Haram sun dasa nakiyoyin a kan hanya tare da shiga garin Marte da kayan farar hula

- A ranar Lahadi ne COAS ya bai wa dakarun kasar nan wa'adin kwato garin Marte daga hannun 'yan ta'adda

Rahotanni sun nuna cewa dakarun sojin kasar Najeriya sun tarwatsa wasu nakiyoyi da Boko Haram suka saka a hanya mai zuwa Marte ta jihar Borno a matsayin tarkon halaka sojoji.

Hakan yana zuwa ne kasa da sa'o'i 48 bayan babban hafsan sojan kasa, Manjo Janar Ibrahim Attahiru ya bai wa dakarun wa'adain kwato Marte daga hannun mayakan ta'addancin.

Kamar yadda jaridar PRNigeria ta bayyana, banda manyan nakiyoyin da Boko Haram suka saka, 'yan ta'addan sun saje da farar hula a Marte don hana soji kai musu harin bama-bamai ta jiragen yaki.

KU KARANTA: Mun zuba soyayya da mijin yayata, yanzu haka ya dirka min ciki, Budurwa na son shawara

Nasara daga Allah: Sojin Najeriya sun tarwatsa nakiyoyin da Boko Haram suka sa a Marte
Nasara daga Allah: Sojin Najeriya sun tarwatsa nakiyoyin da Boko Haram suka sa a Marte. Hoto daga @BBCHausa
Asali: Twitter

Idan za mu tuna, COAS, manjo janar Ibrahim Attahiru ya baiwa rundunar sojin Operation Lafiya Dole sa'o'i 48 da su yi gaggawar kwato Marte daga hannun 'yan Boko Haram sannan su yi gaggawar kwace garuruwa irinsu Kirenowa, Kirta, Wulgo, Chikingudo dake karkashin karamar hukumar Marte da Ngala dake jihar Borno.

Attahiru ya bayar da wannan umarnin ne a ranar Lahadi yayin yi wa sojojin Najeriya na Super Camp 9 jawabi a Dikwa, The Nation ta tabbatar.

KU KARANTA: Ka yi murabus idan ba za ka iya shawo kan matsalar tsaro ba, CSO 43 ga Buhari

A wani labari na daban, daruruwan jama'a sun shiga sarkakiya a birane da kauyuka bayan mayakan Boko Haram sun fatattaki rundunar sojin Najeriya da ke karamar hukumar Marte ta jihar Borno kusan mako daya da ya gabata.

Majiyoyi sun tabbatarwa da Daily Trust cewa mayakan ISWAP sun kafa tutocinsu a wurare daban-daban da suka hada da wurin zama a sabuwar Marte da Kirenowa, manyan biranen karamar hukumar.

A ranar Lahadi, shugaban rundunar sojin, Manjo Janar Ibrahim Attahiru sun bada sa'o'i 48 ga rundunar Operation Lafiya Dole domin kwato Marte daga hannun 'yan ta'addan Boko Haram.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: