Tawagar samu gyaran wutar lantarki a Borno ta ci karo da nakiyar da ISWAP suka dasa

Tawagar samu gyaran wutar lantarki a Borno ta ci karo da nakiyar da ISWAP suka dasa

- Biyo bayan lalata wutan lantarki a jihar Borno, an sake harar motan masu gyaran wutan

- Masu gyaran sun ci karo da wani abin fashewa da ake zargin 'yan kungiyar ISWAP ne suka dasa

- Jihar Borno na iya kokarinta wajen ganin ta maido da wutan lantarki nan ba da jimawa ba

Wata mota dauke da ma’aikatan wutar lantarki da dama da kuma wani jami’in tsaro sun ci karo da wani abin fashewa a safiyar Asabar din nan a jihar Borno, Arewa maso Gabashin Najeriya, HumAngle ta ruwaito rahoto.

Wadanda lamarin ya rutsa da su na daga cikin tawagar da ke aikin dawo da wutar lantarki a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, bayan da kungiyar ISWAP ta lalata wata hasumiyar wuta a sanannen yankin Mainok da ke kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

Sun lalata hasumiyoyin wutan lantarki da dama yayin da Kamfanin Yada Wutan lantarki na Najeriya (TRCN). ke gyara wanda ya lalace mai karfin 330kV.

KU KARANTA: 2023: Matasan Najeriya sun tara N10m don sayawa Tinubu tikitin takarar shugaban kasa

Tawagar gyaran wutar lantarki a Borno ta ci karo da nakiyar da ISWAP suka dasa
Tawagar gyaran wutar lantarki a Borno ta ci karo da nakiyar da ISWAP suka dasa Hoto: The Nation
Asali: UGC

Ba a san yanayin da wadanda abin ya shafa ba ke ciki ba har zuwa lokacin wannan rahoton.

Yankin Mainok ya yi kaurin suna wajen ta'addancin ISWAP, gami da kafa shingayen bincike inda suke satar matafiya da kai hare-hare kan jami’an tsaro.

Tare da goyon bayan Gwamnatin Jihar Borno, TRCN ta shirya don hanzarta maido da wutar lantarki zuwa Maiduguri da kewaye, biyo bayan lalacewar manyan hasumiyoyinta T159, T160 da T161 na 330 Kilo Volt (KV) daga Damaturu zuwa Maiduguri.

Rusa hasumiyar wutar lantarki da dasa IED na iya zama wani bangare na shirin kungiyoyin da ke yakar tattalin arzikin Maiduguri.

KU KARANTA: Jami'an tsaro sun fara sintirin ceton 'yan matan makarantar da aka sace a Zamfara

A wani labarin, Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta ce duk da tabbaci daga gwamnatin tarayya cewa za ta kawo karshen ‘yan bindiga da sace-sacen mutane; rayukan 'yan Najeriya na kara shiga cikin hadari, The Cable ta ruwaito.

Taron na mayar da martani ne kan batun sace-sacen mutane, musamman sace 'yan makaranta mata 317 daga Makarantar Sakandaren 'Yan Mata ta Gwamnati dake Jangebe a karamar hukumar Talata-Mafara, a jihar Zamfara.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel