Kwana Ya Kare: Tsohon Sanata daga Jihar Borno Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- An tabbatar da rasuwar tsohon sanatan Borno ta Tsakiya, Sanata Kaka Mallam Yale a ranar Juma'a, 28 ga watan Agustan 2026
- Dansa mai suna Ibrahim Yale ya bayyana cewa mahaifin na su ya rasu ne a asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri da ke jihar Borno bayan fama da jinya
- An gudanar da sallar jana'izar da misalin karfe 2:00 na rana bayan idar da sallar Juma'a, inda aka ga manyan jiga-jigai daga ciki da wajen jihar Borno
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Borno, Nigeria - Tsohon Sanatan da ya wakilci mazabar Borno ta Tsakiya a Majalisar dattawan Najeriya, Kaka Mallam Yale, ya riga mu gidan gaskiya bayan fama da rashin lafiya.
Rahotanni sun bayyana cewa Sanata Kaka Yale ya rasu ne a safiyar Juma’a, 28 ga watan Agusta, 2026 a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri da ke birnin Maiduguri na jihar Borno yayin da yake karbar magani.

Source: Facebook
An sanar da rasuwar Sanata Kaka Yale
Daya daga cikin ’ya’yansa, Ibrahim Yale, ne ya tabbatar wa da jaridar PUNCH da rasuwar mahaifinsu a wata tattaunawa ta wayar tarho da aka yi da shi ranar Juma’a.
“Eh, ni ne dan cikinsa, mahaifinmu, Kaka Yale, ya rasu a yau (Juma’a),” in ji shi.
Sanata Kaka Mallam Yale ya wakilci mazabar Borno ta Tsakiya a Majalisar Dattawa daga shekarar 2007 zuwa 2011 karkashin jam’iyyar ANPP.
Rasuwar tasa ta jawo jimami a Jihar Borno, musamman tsakanin al’ummar Borno ta Tsakiya da waɗanda suka yi aiki tare da shi a lokacin da yake majalisar dokoki.
An yi jana'izar marigayi Sanata Yale
Rahotanni sun nuna cewa an gudanar da sallar jana'izar marigayi tsohon sanatan a babban masallaci, Central Masjid da ke cikin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
An gudanar da sallar jana'izar da misalin karfe 2:00 na rana bayan idar da sallar Juma'a, inda aka ga manyan jiga-jigai daga ciki da wajen jihar Borno da dumbin mutane sun halarta.
Daga cikin wadanda suka je wurin jana'izar akwai mai girma gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum da tsohon babban hafsan rundunar sojin kasa ta Najeriya, Janar Tukur Yusuf Buratai (mai ritaya).

Source: Facebook
Tuni dai aka yi wa Sanata Mallam Yale sutura tare da kai shi makwancinsa kamar yadda addinin musulunci ya tanada.
Mutanen jihar Borno sun masa addu'a tare da fatak Allah Ya sa Aljannatul Firdausi ta zama makoma a gare shi.
Jigon APC, Hamza Darma ya rasu
A wani labarin, kun ji cewa dattito kuma fitaccen dan siyasa a jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya, Alhaji Hamza Darma ya riga mu gidan gaskiya.
Mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Barau I. Jibrin ya tabbatar da rasuwar dattijon a wata sanarwa da ya fitar.
Barau ya mika sakon ta'aziyya ga iyalansa, yana mai bayyana cewa rasuwar Alhaji Hamza Darma babban rashi ne ga Kano da ma Najeriya baki daya.
Asali: Legit.ng

