Nan babu dadewa zaka dawo jam'iyyar APC, Zulum ga Gwamnan Bauchi
- Gwamna Zulum na jihar Borno ya ce nan babu dadewa takwaransa na jihar Bauchi zai koma APC
- Zulum ya sanar da hakan ne yayin da yaje gagarumin bikin saka harsashin ginin sabon gidan gwamnatin Bauchi
- Gwamnan Bornon ya bayyana irin cigaban da ake samu a yankin a karkashin kungiyar gwamnonin arewa maso gabas
Nan babu dadewa gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed zai koma jam'iyyar APC, cewar gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum.
Gwamna Zulum ya sanar da hakan ne a ranar Talata yayin bikin saka harsashin sabon gagarumin gidan gwamnatin jihar Bauchi da zai lamushe N6.3 biliyan, Channels TV ta wallafa.
"Bari in sake nuna godiyata ga takwarana gwamnan jihar Bauchi da sauran takwarorina na arewa maso yamma da suke bani goyon baya mai matukar yawa.
KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun kutsa FCT, sun bindige mai juna biyu tare da sace mijinta
"Rikici daya da nake yi da takwarana gwamnan jihar Bauchi shine kin dawowa jam'iyyar APC. Da izinin Allah nan babu dadewa zai dawo cikinmu. Ina goyon bayan shi," Zulum yace.
Zulum wanda shine shugaban kungiyar gwamnonin arewa maso gabas yayi bayani a kan cigaban da yankin arewa maso gabas ke samu.
Ya ce kungiyar tayi matukar kokari wurin sauya alkiblar yankin a watanni kalilan bayan kafa ta kuma zata cigaba da samar da sauye-sauye.
Ya kara da sanar da cewa kungiyar na tunanin kafa bankin arewa maso gabas wanda zai dinga samar da kudade ga kananan sana'o'in matasa, mata da masu kananan karfi.
KU KARANTA: Rashin tsaro: PDP na zargin APC da kitsa yadda za ta kwace jihar Zamfara
A wani labari na daban, Bello Matawalle, gwamnan jihar Zamfara, ya ce ya shirya tsaf domin yin murabus idan hakan zai kawo karshen rashin tsaro a jihar.
Gwamnan ya sanar da hakan ne a wani shirin siyasarmu a yau wanda gidan talabijin na Channels TV ya shirya a ranar Laraba.
Ya ce: "Ban damu ba. Idan na san murabus dina a matsayin gwamna zai sa jama'a su kwanta bacci idanunsu biyu rufe, zan sauka daga mulkin."
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng