Abin Boye Ya Fito: Dalilin da Ya Sa Tinubu Ya Shilla zuwa Nahiyar Turai
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tashi daga Najeriya zuwa Turai domin hutun shekara na makonni uku
- Sunday Dare ya ce hutun ya dace bayan watanni da shugaban kasar ke yanke manyan shawarwari kan tsaro da tattalin arziki
- Ya ce Tinubu zai ci gaba da karɓar rahotannin gwamnati da muhimman bayanai duk da cewa yana hutu a kasashen wajen
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bar ƙasar zuwa Turai domin yin hutun makonni uku, a matsayin wani ɓangare na hutun shekara da yake gudanarwa.
Tinubu ya samu rakiyar wasu manyan jami’an gwamnati da jami’an tsaro zuwa filin jirgi, yayin da ya fara hutun a daidai lokacin da harkokin siyasa ke ƙara ɗaukar zafi gabanin zaɓen 2027.

Source: Facebook
Dare ya ce hutun zai ba Tinubu damar yin caji
Sunday Dare, mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan yaɗa labarai da sadarwar jama’a, ya bayyana hutun a matsayin wanda shugaban ya cancanta ya samu, cewar rahoton jaridar The Punch.
Da yake magana da manema labarai a filin jirgin sama, Dare ya ce Tinubu ya shafe watanni yana fuskantar muhimman batutuwan ƙasa tare da yanke manyan shawarwari.
Ya ce shugaban ya mayar da hankali kan batutuwan tsaro, tattalin arziki da sauran harkokin gudanar da ƙasa, jaridar Daily Trust ta kawo labarin.
“A wannan lokaci, yana da muhimmanci shugaban ƙasa ya samu damar caja batirinsa,” in ji Dare.
Ya ce kamfen na 2027 na gabatowa
Dare ya ce hutun ya zo ne a lokacin da lokacin kamfen na zaɓen 2027 ya fara ɗaukar hankali. A cewarsa, ana gab da shiga watanni huɗu zuwa shida na tsananin yakin neman zaɓe, yayin da harkokin mulki za su ci gaba da gudana.
Ya ce saboda yawan ayyukan da shugaban ya gudanar cikin watanni shida ko bakwai da suka gabata, hutun zai ba shi damar shirya kansa domin sabon yanayin siyasar da ke tafe.

Kara karanta wannan
Shirin dawo da tallafin man fetur ya firgita shugaban APC, ya fadi illar shirin Atiku
“Shugaban ya shafe watanni shida ko bakwai yana gudanar da harkokin ƙasa. Mun ga manyan sauye-sauye da kuma manyan shawarwari kan tsaro, tattalin arziki da sauran al’amuran ƙasar,” in ji shi.
Tinubu zai ci gaba da samun rahotannin gwamnati
Dare ya bayyana cewa duk da kasancewar shugaban a hutu, ba zai katse hulɗarsa da harkokin gwamnati gaba ɗaya ba.
Ya ce Tinubu zai ci gaba da karɓar rahotanni daga ministoci, shugabannin hukumomin tsaro da sauran jami’an da ke kula da muhimman al’amuran ƙasa.
“Ko da yake yana tafiya hutu, mun san cewa zai ci gaba da kula da harkokin ƙasa a kullum,” In ji shi
Ya ƙara da cewa shugaban zai karɓi bayanai da rahotanni daga ministocinsa da shugabannin rundunonin tsaro, da kuma sauran jami’an da ke da hannu wajen yanke muhimman shawarwari.
Dare ya ce hakan zai tabbatar da cewa tafiyar da harkokin gwamnati ba za ta tsaya ba yayin da shugaban ke hutun shekara a Turai.

Source: Facebook
Atiku ya soki Tinubu kan tafiya hutu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Atiku Abubakar, ya bayyana rashin amincewarsa da matakin Shugaba Bola Tinubu na tafiya Turai domin hutu na mako uku.
Atiju ya ce aakwai bambanci tsakanin tafiyar ɗan ƙasa mai zaman kansa da kuma nauyin da ke kan shugaban da ke jagorantar ƙasar.
Asali: Legit.ng
