Da duminsa: Mayakan ISWAP da sojin Najeriya ana musayar wuta a Dikwa, Borno

Da duminsa: Mayakan ISWAP da sojin Najeriya ana musayar wuta a Dikwa, Borno

- Labari da duminsa da ke zuwa shine na farmakin da mayakan ISWAP suke kaiwa yanzu a Dikwa

- Ana ta musayar wuta tsakanin 'yan ta'addan da sojojin wadanda ke samun tallafi daga jiragen yaki

- Wannan ne hari na uku da mayakan ISWAP suka kaiwa garin Dikwa a 2021

Ma'aikatan tallafi da ke taimakon 'yan gudun hijira a halin yanzu suna cikin wani hali bayan 'yan ta'adda sun kaddamar da hari a Dikwa.

Mayakan ta'addancin duk 'yan ISWAP ne, wani sashe na 'yan ta'adda da suka rabu da Boko Haram.

Harin yana zuwa ne bayan kwanaki kadan da shugaban rundunar sojin kasa ya kai ziyara babban sansanin sojin da ke yankin.

KU KARANTA: Mayakan ISWAP sun kaiwa kwamandan Operation Lafiya Dole farmaki a Borno

Da duminsa: Mayakan ISWAP sun ragargaza jama'a a garin Dikwa
Da duminsa: Mayakan ISWAP sun ragargaza jama'a a garin Dikwa
Asali: Original

Dikwa tana da nisan kilomita 90 gabas da Maiduguri, babban birnin jihar Borno da ke arewa maso gabas din Najeriya, HumAngle ta ruwaito.

Lamarin ya kazanta domin karar makamai da tashin bindiga ake ji yayin da sojoji ke samun taimako ta jiragen yaki.

Wannan ne farmaki na uku a cikin shekarar 2021 da ISWAP suka kaiwa Dikwa. A harin da ya gabata, mayakan ta'addancin sun sanar da mazauna yankin za su ddawo a ranar 28 ga watan Fabrairu.

KU KARANTA: Kagara: 'Yan bindiga basu tausayi ko tsoro, sun ce alkawarinsu gwamnati ta karya, Hauwa

A wani labari na daban, tsohon gwamnan jihar Osun kuma ministan cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola a ranakun karshen mako ya musanta labarin da ke yawo na cewa ya samu albashinsa na watanni 96 a sirrance a lokacin da yayi shugabancin jihar.

Ya kwatanta rahoton da labarin kanzon kurege wanda aka hada shi domin zubar da nagartar Ogbeni Rauf Aregbesola.

A wata takarda da hadimin Aregbesola na yada labarai, Soka Fasure ya fitar, ya ce rahoton da ake yaduwa a yanar gizo ya saba dokokin jaridanci, The Nation ta wallafa.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: