'Yan Boko Haram sun sace ma'aikatan jin kai bakwai a Borno
- Yan ta'addan kungiyar Boko Haram sun sace ma'aikatan jin kai guda bakwai a Dikwa
- Hakan na zuwa ne bayan harin da yan ta'addan suka kai garin bayan fafatawa da sojoji
- Yan ta'addan sun kuma kone asibitoci da gine-ginen gwamnati da na kungiyoyi jin kai a Dikwa
Mayakan Boko Haram sun kai hari a karamar hukumar Dikwa a Borno sun sace a kalla ma'aikatan jin kai a Borno, Channels Television ta ruwaito.
Yan ta'addan yayin harin sun kone ofisoshin ma'aikatan jin kai, sun lalata kayayyakin gwamnati da asibitoci mallakar kungiyoyi masu taimakon jama'a, NGOs.
DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun yi barazanar kashe mu, su soya namar mu su cinye, Ɗalibar Jangebe
Wani shaidan ganin ido ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa yan ta'addan sun afka garin misalin karfe 5.30 na yammacin Litinin, kuma sun kwace garin.
Shaidan ya ce sojojin sun kwashe dare suna kokarin kwato garin.
Yan ta'addan sun kai wa sojojin da aka turo daga Ajiri hari a safiyar ranar Talata wadda hakan yasa yan ta'addan suka ci karensu babu babbaka.
Wasu ma'aikatan jin kai da suka yi magana da Channels Television daga garin sun bayyana yadda yan ta'addan suka kone asibitoci da gine-gine mallakar kungiyoyin masu taimakon jama'a.
KU KARANTA: Yanzun nan: 'Yan Boko Haram sun ƙwace Dikwa da dubban mutane cikin garin
Wannan harin na zuwa ne awanni 24 bayan gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya dawo daga garin Dikwa inda ya shafe kwanaki uku.
Zulum ya baro Maiduguri a ranar Laraba, bayan sojoji sun kwato Marte daga hannun yan ta'addan inda ya tafi Dikwa ya tsaya har zuwa ranar Asabar ya kuma kara gaba zuwa Ngala ya koma Maiduguri a ranar Lahadi.
A wani labarin daban, kun ji Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi, NDLEA, ta kama wani mai fataucin miyagun kwayoyi mai shekaru 36 dauke da hodar Iblis da ta kai na Naira biliyan daya.
NDLEA ta ce mai safarar, Nkem Timothy, wanda ya yi basaja a matsayin Auwalu Audu domin yin fataucin kunshin hodar Iblis da nauyinsa ya kai 1.550kg. An yi kiyashin kudinsa ya kai Naira biliyan 1.
Kakakin NDLEA, Femi Babafemi ya ce an kama wanda ake zargin ne yayin da ya ke kokarin zuwa Algeria ta bodar jamhuriyar Nijar.
Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.
Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.
Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu
Asali: Legit.ng