Daga Karshe: 'Yan N-Power da Gwamnatin Tinubu ta Hana Kudadensu Sun Yanke Atiku Za Su Zaba a 2027
- Wata tawaga daga 'yan shirin N-Power ta sanar da goyon bayanta ga tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar
- Wani mamba a kungiyar The Atiku Movement wato AbdulAziz Na'ibi Abubakar ne ya bayyana wannan matsaya
- Wannan goyon baya na zuwa ne a yayin da shirin N-Power ke fuskantar matsaloli da kuma batun bashin N81bn
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
FCT, Abuja - Wata 'tawagar kasa' ta mutanen da suka amfana da shirin N-Power ta bayyana goyon bayanta ga Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC a zaben shekarar 2027.
Wani mai sharhi kan al'amuran yau da kullum kuma mamba a kungiyar The Atiku Movement (TAM), AbdulAziz Na'ibi Abubakar ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Asabar, 29 ga Agusta, 2026.
Kungiyar TAM tana daya daga cikin kungiyoyin da ke goyon bayan tsohon mataimakin shugaban kasar a takararsa ta 2027.

Source: Twitter
Dalilin nuna goyon bayansu ga Atiku
Na'ibi ya rubuta cewa:
"Labari da Dumi-Duminsa: Masu amfana da shirin N-Power miliyan 1.4 sun bayyana goyon bayansu ga Atiku Abubakar gabanin zaben 2027."
Duk da cewa Na’ibi ya yi ikirarin cewa mutane miliyan 1.4 ne suka bayyana wannan goyon baya, Legit.ng ba ta sami damar tabbatar da gaskiyar wannan alkaluma ba.
Wannan matsaya na zuwa ne a yayin da jam'iyyun siyasa da 'yan hamayya a fadin Najeriya ke kara zage dantse wajen fito da tsare-tsarensu gabanin zaben.
Matsalolin da suka dabaibaye shirin N-Power
Shirin N-Power, wanda yana daya daga cikin shirye-shiryen rage radadin talauci da aka kaddamar a karkashin mulkin marigayi tsohon Shugaba Muhammadu Buhari a watan Yunin 2016, an tsara shi ne domin rage matsalar rashin aikin yi tsakanin matasa a Najeriya.
Shirin, wanda gwamnatin jam'iyyar APC ta kafa, ya gudanar da rukunoni daban-daban da suka hada da Batch A, B, da C.
Wadanda suka kammala jami'a suna samun alawus na N30,000 kowane wata na tsawon shekara guda ko fiye da haka, yayin da wadanda ba masu digiri ba ke samun N10,000 a kowane wata.
A watan Oktoban 2023, gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin na N-Power sannan ta ba da umarnin gudanar da bincike na gaggawa.
Ana bincike kan shirin N-Power
Wata sanarwa da Shugaban Shirin na Kasa, Akindele Egbuwalo, ya saka wa hannu a madadin tsohuwar minista Betta Edu, ta bayyana cewa an samu tsaiko da fitar da kudaden da ba su dace ba ga mutanen da zamansu a shirin ya kare.
Sanarwar ta ce, kamar yadda jaridar Guardian ta wallafa:
"Kwanan nan, mun gano wasu mutane da ke cin gajiyar shirin wadanda zamansu ya kare tun 2022 amma har yanzu suna cikin tsarin kuma suna tsammanin karbar kudi daga gwamnati."
Sanarwar ta kuma kara da cewa wasu mutanen na karbar kudin alawus din kowane wata alhali ba sa zuwa wuraren aikinsu, yayin da wasu kuma suka samu sauran ayyukan yi amma suke ci gaba da karbar kudin shirin.
Gwamnati na bin bashin N81bn da ba a warware ba

Kara karanta wannan
'Ban da Atiku,' Dan takara 1 da ya bugu kirji kan shi kadai zai iya maido tallafin mai
A watan Yulin 2025, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, ya shiga tsakani domin gudanar da tattaunawa tsakanin jami'an gwamnatin tarayya, masu korafi daga shirin, da lauyansu, Abba Hikima.
Masu amfana da shirin na N-Power sun yi barazanar shigar da kara kotu kan zargin rashin biyan bashin alawus na shekarar 2022 da 2023 da ya kai N81bn.
Bayan gudanar da tattaunawar, Jibrin ya bayyana cewa masu korafin sun amince su dakatar da shirin tafiya kotu bayan samun tabbaci daga gwamnati cewa za a biya su kudadensu.
Kamar yadda jaridar The Cable ta wallafa, ya amince cewa gwamnatin da ta gabata ce ta bar wannan bashi, amma gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta jajirce wajen biyan kudaden a karkashin tsarin Renewed Hope.
A cikin wannan yanayi na rashin warware batun kudade da kuma rashin tabbas a fannin siyasa ne wannan tawaga ta N-Power ta bayyana goyon bayanta ga Atiku.
Wanda ya tantance Salisu Ibrahim, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

