Yanzu haka, mayakan Boko Haram sun budewa Dikwa da Gajiram wuta
- Labarai masu zafi da ke zuwa a halin yanzu shine na farmakin da Boko Haram suke kaiwa Gajiram da Dikwa
- Da tsakar ranar Talata ne mayakan ta'addancin suka bar garin Dikwa bayan kwace garin da suka yi ranar Litinin
- An gano cewa mayakan sun sake komawa garin Dikwa da Gajiram da ke Nganzai a yammacin Talata
Wasu mayakan ta'addancin da ake zargin na Boko Haram kamar yadda majiyoyi suka tabbatar a halin yanzu suna kai farmaki karamar hukumar Dikwa ta jihar Borno bayan tserewa da suka yi wurin karfe 12 na ranar Talata.
Kamar yadda aka gano, sun kwace garin Dikwa da yammacin ranar Litinin.
Kamar yadda Vanguard ta wallafa, hakan ce ke faruwa yanzu haka a garin Gajiram da ke karamar hukumar Nganzai ta jihar Borno, majiyoyi masu karfi suka tabbatar.
KU KARANTA: Satar 'yan makaranta: Wasu jama'a ne ke yunkurin tozarta wannan gwamnatin, Sirika
Karin bayani na nan tafe...
KU KARANTA: Zan halarci mukabalar da aka shirya mana da malaman Kano, Sheikh Kabara
A wani labari na daban, tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule lamido, ya ce Salihu Tanko Yakasai, tsohon hadimin Ganduje na jihar Kano, yafi Femi Adesina da Garba Shehu jarumta.
An kama Salihu a ranar Asabar bayan ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi murabus sakamakon yawaitar rashin tsaro a kasar nan.
Labarin damke shi da aka yi ya karade gari yayin da Ganduje ya sanar da cewa ya sallame shi daga aiki, Daily Trust ta wallafa.
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng