Jihar Benue
Rahotanni sun kawo cewa cibiyoyin lafiya a Najeriya sun tabbatar da cewar masana na nan suna gudanar da bincike a kan wata bakuwar cuta a jahar Benue.
Idan ajali ya yi kira, ko ba ciwo sai an je, kamar yadda yan Hausa suke fada, a nan ma wata mata mai suna Ngodoo ce ta gamu da ajalinta bayan ta yanke jiki ta fadi a lokacin da take tsaka da raba fada tsakanin yaranta biyu.
A yayin da ake fama da bullar cutar zazzabin Lassa a Najeriya, wata sabuwar annoba ta bayyana a jahar Benuwe, yankin Arewa maso tsakiyan Najeriya, kuma har ta halaka akalla mutane hudu.
Jim kadan bayan kotun kolin Najeriya ta tabbatar da nasarar Gwamna Samuel Ortom a matsayin gwamnan jihar Benuwai, ya gangara coci don addu'a tare da godiya ga Ubangiji...
Kamar PDP ta zuba ruwa a kasa ta sha bayan nasara a Kotu Benuwai. Nasarar Gwamna Ortom ta sa ‘Yan Jam’iyyar PDP farin ciki a Benuwai
Kotun koli a yau Talata, 21 ga watan Janairu ta tabbatar da zaben gwamna Samuel Ortom na jihar Benue. Ta kuma yi watsi da karar dan takarar APC.
Kotun koli ta shirya yanke hukunci kan karar da aka daukaka kan zabukan gwamna da ya gabata a jihohin Adamawa da Benue a yau Talata, 21 ga watan Janairu. Kotun za ta fara sauraron karar ne da misalin karfe 2:00 na rana.
Jami’an hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC sun dira jahar Benuwe inda suka yi ram da akawun majalisar dokokin jahar, Torese Agena a kan zarginsa da hukumar take yi da satar kudi naira miliyan 2
Mutane da dama sun kone kurmus bayan wata babbar tankar dakon man fetir ta kama d wuta a kauyen Agudo dake jahar Benuwe a ranar Talata, 14 ga watan Janairu, haka zalika gidaje da dama sun kone.
Jihar Benue
Samu kari