Tirkashi: Mujiya ta kai wa Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue hari a coci

Tirkashi: Mujiya ta kai wa Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue hari a coci

- Bayan samun nasarar Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai a kotun koli, ya gangara don godiya ga Ubangiji a coci

- Amma sai ga wata mujiya a daren ranar Talata din har cikin cocin kuma ta nufi gwamnan babu kakkautawa

- Kokarin wasu matasa da ke cocin ne ya hana mujiyar sauka a tsakar kan Gwamnan wanda aka jaddada nasarar shi a ranar

Jim kadan bayan kotun kolin Najeriya ta tabbatar da nasarar Gwamna Samuel Ortom a matsayin gwamnan jihar Benuwai, ya gangara coci don addu'a tare da godiya ga Ubangiji.

Amma a cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG), Makurdi, sai wani abin firgici da mamaki ya faru. Wata mujiya ce wacce ake zaton ta sihiri ce ta shigo cocin da daren kuma a dai-dai lokacin da Ortom ya gurfana don addu'o'i.

Kamar yadda jaridar Daily Post ta ruwaito, Ortom ya je cocin ne don godiya ta musamman ga Ubangiji a kan nasarar da ya samu amma sai ga mujiya ta shigo.

KU KARANTA: Mata ta bayyana yadda Fasto ya karbi mahaifar dan da ta haifa da ya sanya har yanzu baya iya magana da tafiya

Wani ganau ba jiyau ba mai suna Prince Tordue Abe, ya bada labarin yadda mujiyar ta bayyana a cocin a dai-dai lokacin da Gwamnan ke godiya a kan nasarar shi kuma ta nufi gwamnan ba kakkautawa.

Amma wasu matasa da ke cocin sun hanzarta kama mujiyar wacce ta so sauka a tsakar kan gwamnan.

Mutane da yawa da ke wajen sun dinga mamakin yadda aka yi mujiyar ta shigo cocin da yadda ta tunkari gwamnan a tsakiyar kan shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel