Allah kare: Jama’a sun kone kurmus yayin da tanka makare da man fetir ta kama da wuta

Allah kare: Jama’a sun kone kurmus yayin da tanka makare da man fetir ta kama da wuta

Mutane da dama sun kone kurmus bayan wata babbar tankar dakon man fetir ta kama d wuta a kauyen Agudo dake jahar Benuwe a ranar Talata, 14 ga watan Janairu, haka zalika gidaje da dama sun kone.

Jaridar The Nation ta ruwaito lamarin ya faru ne a kauyen Agudo yana nan ne a cikin karamar hukumar Tarka a kan babbar hanyar Makurdi zuwa Gboko, a daidai wata kwanar mutuwa. Nan ne garin ministan Buhari, George Akume.

KU KARANTA: Gwamnatin Kaduna ta garkame bankuna guda 3 saboda kin biyan haraji

Wani shaidan ganau ba jiyau ba, Justice Anzembe ya bayyana ma majiyar Legit.ng cewa motar tankar man fetirin makare da mai tana kan hanyar ta na zuwa Gboko ne daga Makurdi, amma sai direban motar ya yi wautar bin ta cikin wasu ciyaye da ake konawa a kan hanyar, daga nan motar ta kama da wuta.

Sanannen al’ada ce ga jama’an jahar Benuwe inda suke kona daji da ciyayi domin farautar namun daji a lokacin rani, sai dai a wannan karo wutar ta tafka musu mummunar barna inda ta babbaka gidaje da kadarori da dama.

Zuwa lokacin tattara wannan rahoto lamarin ya haifar da cunkoson ababen hawa a kan titin.

A wani labarin kuma, Allah Sarki, wasu miyagu yan bindiga sun sace tare da garkuwa da wasu malaman makarantar firamari guda biyu a kauyen Avbiosi na karamar hukumar Owan ta yamma a jahar Edo.

Maharan sun dauke malaman makarantar ne a ranar Litinin, 13 ga watan Janairu yayin da suke tsaka da koyarwa a makarantar firamarin gwamnati na Obi Camp, malaman sun hada da Dada Okun da Esther Alabi.

Sai dai jim kadan bayan sace malaman, yan bindigan sun tuntubi iyalansu, inda suka nemi a biyasu kudin fansa naira miliyan 1 kafin su sake su, amma daga bisani suka kara kudin zuwa naira miliyan 15.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: