Akpabio Ya Yi wa Oshiomhole Shagube kan 'Bidiyonsa' Yana Yi wa Budurwa Tausa a Jirgi
- Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya yi shagube kan bidiyon da ya yaɗu na Sanata Adams Oshiomhole
- An gano wani bidiyon Oshiomhole da wata budurwa a jirgi da ya yadu wanda ya jawo magana a fadin kasar
- Akpabio ya ce Sanata Simon Lalong ya sanar da shi batun, kuma Majalisar Dattawa ta yi watsi da bidiyon saboda zargin an ƙirƙire shi da AI
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya yi barkwanci kan bidiyon Sanata Adams Oshiomhole.
A bidiyon da ya yaɗu, ana zargin ya Oshiomhole yana tausa wa ƙafar wata mata a cikin jirgi mai zaman kansa.

Source: UGC
Yayin zaman majalisar, a wani bidiyo da AIT ta wallafa, Akpabio ya ce bai so ya kauce daga batun da suke tattaunawa ba.
Akpabio ya taba Sanata OshiomholeaAkoA
Ya ce da farko Majalisar Dattawa ta yi watsi da bidiyon ne saboda ta yi zargin cewa fasahar ƙirƙirar hotuna da bidiyo ta AI ce ta samar da shi.
Sai dai ya ce da ya yi tambaya game da hoton da ya nuna ɗaya daga cikin sanatocin yana cikin jirgin sama yana tausa ƙafar wata budurwa.
Kalaman nasa sun jawo dariya a tsakanin sanatocin da ke zauren majalisar, ciki har da shi kansa Akpabio.
Akpabio ya ce:
"Sanata Oshiomhole, abokinka, babban abokinka Sanata Lalong, ya zo ya ba ni bayanin tsaro. Ya ce mun yi watsi da saƙon ne saboda mun yi tunanin AI ce ta ƙirƙire shi.
"Amma idan kuna da wata sabuwar hujja, muna da ƙorafi a gabanmu, za mu iya duba shi idan ba AI ba ne."

Source: Facebook
Akpabio ya tayar da kura a majalisa
Kalaman Akpabio sun yi nuni da wani bidiyo da ya yaɗu sosai a farkon watan Fabrairun 2026.
Bidiyon ya nuna wani mutum mai kama da Sanatan Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole, yana zaune a cikin wani jirgin sama mai zaman kansa yayin da wata mata ta ɗora ƙafafunta a cinyarsa, kuma ya bayyana kamar yana taɓawa ko tausa ƙafafunta.
Bidiyon ya jawo suka da ba'a daga jama'a musamman saboda halin matsin tattalin arzikin da Najeriya ke ciki.
Da yake mayar da martani kan bidiyon, Sanata Adams Oshiomhole, ta bakin mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Oseni Momodu, ya musanta sahihancinsa.
Ya bayyana shi a matsayin bidiyon bogi da aka ƙirƙira ta amfani da AI domin bata masa suna da kuma muzanta shi.
Bangaren Oshiomhole ya kuma yi Allah wadai da yaɗa bidiyon, yana mai cewa hakan cin zarafin yanar gizo ne.
Ya bukaci jama'a su tabbatar da sahihancin duk wani abu da suka gani a intanet kafin su yaɗa shi, tare da bayyana cewa ana ƙoƙarin gano waɗanda suka ƙirƙira da kuma yaɗa bidiyon.
'Halin da na shiga bayan tsige ni: - Oshiomhole
Mun ba ku labarin cewa tsohon shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole ya bayyana irin halin kadaicim da ya tsinci kansa a ciki bayan an tsige shi a 2020.

Kara karanta wannan
Baban Chinedu ya yabi nagartar Pantami amma ya fadi wurin da za a nakasa shi a siyasa
Sanata Oshiomhole mai wakiltar jihar Edo ta Arewa ya ce mutane sun gudu sun bar sa lokacin da ya rasa matsayinsa a jam'iyyar APC.
Ya ce gwamnan Ribas a wancan lokacin, Nyesom Wike ne kadai ya jawo shi a jiki, ya gayyace shi zuwa Fatakwal kuma ya ba shi lambar yabo.
Asali: Legit.ng

