Yanzu Yanzu: Da karfe 2 na rana Kotun koli za ta yanke hukunci kan zabukan gwamnan Adamawa da Benue
Kotun koli ta shirya yanke hukunci kan karar da aka daukaka kan zabukan gwamna da ya gabata a jihohin Adamawa da Benue a yau Talata, 21 ga watan Janairu.
Kotun za ta fara sauraron karar ne da misalin karfe 2:00 na rana.
Emmanuel Jime, wanda ya kasance dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kalubalantar nasarar Samuel Ortom na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a matsayin wanda ya lashe zaben.
Kwamitin mutum bakwai na kotun kolin ya ce bayan lauyoyin jam’iyyar sun gama muhawararsu, za a zartar da hukunci a yau Talata.
Hakazalika a jihar Adamawa, dan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kalubalantar nasarar Umaru Fintiri (Adamawa) na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
KU KARANTA KUMA: An kashe mutane 3 a rikicin makiyaya da manoma a garin Kogi
A baya Legit.ng ta rahoto cewa alkalai masu shari'a sun tabbatar da Simon Bako Lalong matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Plateau.
Kotun ta raba gardamar ne bayan watanni goma da hukumar gudanar da zabe INEC ta alantashi matsayin zakaran zaben 9 ga Maris, 2020.
Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da dan takararta Jeremiah Useni, sun shigar da kara kotu ne domin kalubalantar nasarar APC a zaben.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng