Harin Benue: Wata kungiya ta ba makiyaya wa’ adin sa’ a 48 su bar jahar ko su dandana kudarsu
Biyo bayan tsoro da aka shiga kan ci gaba da kai hare-hare da kisan bayin Allah da ake yi a jahar Benue, shugaban kungiyar matasan Tiv na kasa a ranar Asabar ya bukaci matasan Benue yan kabilar Tiv da su dauki matakin kare kansu daga yawan hare-hare da kashe-kashen da ake yi.
Baya ga haka, kungiyar ta ba makiyaya sa’o’i 48 su tattara su bar jahar sannan ta yi barazanar cewa duk wanda ya gani daga cikinsu bayan karewar wa’adin toh za ta kawar dashi nan take.
Zababben shugaban kungiyar na kasa, Mista Timothy Hembaor ya bayyana hakan a wani jawabi da ya bai wa manema labarai a Makurdi, babbar birnin jahar.
Hambaor ya nuna bacin rai cewa bayan kokarin da kungiyar ta yi domin samun zaman lafiya, makiyayan na ci gaba da kaddamar da hare-hare akan manoma yan kabilar Tiv wanda hakan ne ya sa suka yi kira ya matakin kare kai.
KU KARANTA KUMA: Coronavirus: Buhari ya shiga ganawar sirri da Gwamna Sanwo-Olu a fadar Villa
Ya nuna bakin ciki kan kisan mutum 10 a karamar hukumar Kwande da makiyaya suka yi da kuma na Mwaba a karamar hukumar Guma inda aka yiwa matar wani basarake da surukansa shida fyade.
A baya mun ji cewa mata uku ne wadanda suka hada da matar dagaci da surukansa biyu ne ‘yan bindiga suka yi wa fyade a sa’o’in farko na ranar Alhamis, bayan harin da suka kai yankin Mbanyiar da ke karamar hukumar Guma ta jihar Binuwai.
Jaridar daily Trust ta gano cewa maharan sun bayyana ne da miyagun makamai kuma sai suka zagaye gidan basaraken sannan suka yi wa matarsa fyade da surukansa mata biyu.
Basaraken, wanda ya bukaci da a sakaya sunansa, ya sanar da manema labarai cewa ana zargin maharan Fulani ne makiyaya don har kayan abincinsu sai da suka lalata a yayin harin.
Ya bayyana cewa maharan su 11 ne kuma sun iso ne wajen karfe 2 na dare, amma ya samu nasarar tserewa daga garesu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng