Wata bakuwar cuta ta bulla a jihar Benue, ta kashe mutum 15, sama da mutane 100 sun kamu

Wata bakuwar cuta ta bulla a jihar Benue, ta kashe mutum 15, sama da mutane 100 sun kamu

Rahotanni sun kawo cewa cibiyoyin lafiya a Najeriya sun tabbatar da cewar masana na nan suna gudanar da bincike a kan wata bakuwar cuta a jahar Benue.

Chikwe Ihekweazu, darakta-janar na hukumar NCDC, ya fada ma kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a ranar Asabar cewa hukumar na daukar matakan magance cutar wanda aka ce ya kashe mutane 15.

Abba Moro, sanata daga Benue, ya bayar da rahoton mutanen da suka mutu a zauren majalisar dattawan. Ya kuma bayyana cewa mutane sama da 100 sun samu cutar.

Wata bakuwar cuta ta bulla a jihar Benue, ya kashe mutum 15, sama da mutane 100 sun kamu
Wata bakuwar cuta ta bulla a jihar Benue, ya kashe mutum 15, sama da mutane 100 sun kamu
Asali: Depositphotos

Sakamakon wasu bayanai daga dakin bincike ya nuna cewa bakuwar cutar ba ta Lassa ba ce.

An tattaro cewa ministan lafiya, Dakta Osagie Ehanire ya bayyana cewa na zargin mutane sun ci wani kifi da suka kana a wani rafi da aka zuba wa guba ne

A cewarsa Hakan na da hatsari matuka ga lafiyar dan Adam.

Osagie ya kara da cewa hukumomin lafiya da ke tashoshin jiragen kasar a shirye suke don ganin an tunkari duk wata cuta da ka iya shigowa kasar.

KU KARANTA KUMA: Bidiyon tsiraici: Maryam Booth ta bayyana gaskiyar lamari

Ministan ya ce bukaci mutane da su kwantar da hankalinsu don har yanzu babu billar cutar coronavirus a kasar.

A wani labari na daban, mun ji cewa Faston kasar Ghana mai abun mamaki mai suna Angel Bishop Daniel Obinim ya kaddamar da wani man waraka mai yakar cutar Coronavirus.

Shugaban cocin International God's Way din ya kaddamar da wannan man warakar ne a ranar Lahadi da ta gabata yayin da yake wa'azi a cocin.

Kamar yadda ya ce, barkewar cutar Coronavirus din a kasar China ta dame shi kuma yana tsoron cewa cutar za ta iya sauka a kasar Ghana. A don haka ne ya yanke shawarar kirkiro man warakan don yakar cutar.

Ya ce za a shafa man a duk jiki ne don bada kariya daga cutar.

Ana siyar da man ne kan N13,400 kuma sashen aljannan na FDS ta aminta da shi kamar yadda Obinim ya bayyana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng