Malaysia Ta Shirya Korar Duk Wani Dan Isra'ila da Aka Gano a Kasarta Nan Take
- Firaministan Malaysia, Anwar Ibrahim, ya bayyana cewa duk wani ɗan Isra'ila da aka gano yana cikin ƙasar za a kore shi nan take
- Matakin ya biyo bayan rahotannin cewa wasu masu shiga aikin fasaha sun shiga Malaysia da fasfo na wata ƙasa duk da kasancewarsu 'yan Isra'ila
- Hukumomin shige da fice da tsaro sun fara bincike, inda suka tantance takardun baƙi 266 daga ƙasashe 40 yayin da Malaysia ta sake jaddada matsayinta kan Isra'ila
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Malaysia - Yan Isra'ila da ke zama a Malaysia za su fuskanci matsala bayan matakin kasar ke shirin dauka kansu domin inganta tsaro.
Firayim ministan Malaysia, Anwar Ibrahim, ya sanar cewa duk wani ɗan Isra'ila da aka gano yana cikin ƙasar za a kore shi nan take saboda Malaysia ba ta amince da Isra'ila ba.

Source: Getty Images
Ya bayyana hakan ne bayan rahotannin da suka bazu a shafukan sada zumunta cewa wasu masu shiga aikin fasaha mai suna Network School sun shiga Malaysia da fasfo na wata ƙasa, cewar Israel National News.
Zargin da Malaysia ke yi wa Isra'ilawa
An ce aikin yana gudana ne a yankin Forest City da ke jihar Johor a kudancin Malaysia, kuma wasu mahalarta ana zargin suna da zama 'yan Isra'ila tare da wata ƙasa.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai, Ibrahim ya ce gwamnatinsa ba za ta yi sassauci ba kan batutuwan tsaron ƙasa da kuma matsayinta game da Isra'ila.
Ya ce idan bincike ya tabbatar da cewa rahotannin gaskiya ne, za a kori mutanen nan take, kuma hukumomin da abin ya shafa sun riga sun fara bincike.

Source: Getty Images
Matsalar da ke tsakanin Isra'ila da Malaysia
Firaministan ya sake jaddada cewa Malaysia ba ta amince da kasar Isra'ila a matsayin ƙasa ba, kuma ba ta da hulɗar diflomasiyya da ita, saboda haka ba ta yarda 'yan Isra'ila su zauna a ƙasar, cewar Anadolu Ajansi.
Rahotannin kafafen yaɗa labarai na cikin gida sun ce hukumomin shige da fice da na tsaro sun kai samame wurin aikin, inda suka duba takardun baƙi 266 daga ƙasashe 40 domin tabbatar da sahihancin shigarsu.
Malaysia na daga cikin ƙasashen Musulmi da suka fi nuna adawa da Isra'ila, kuma ta ci gaba da goyon bayan Falasɗinawa a matakin ƙasa da ƙasa tare da tsaurara kalamanta kan Isra'ila tun bayan fara yaƙin Gaza.
Asirin Isra'ila ta tonu a Iran
Mun ba ku labarin cewa wani rahoto ya bayyana yadda Isra'ila ta yi shekaru tana ƙulla alaka da tsohon shugaban Iran Mahmoud Ahmadinejad a asirce.
An ce sun yi tarurrukan sirri a Budapest a shekara 2024 da 2025, inda tsohon shugaban Mossad David Barnea ya hadu da shi.
Rahoton ya nuna cewa shirin ya ci tura ne bayan jami'an IRGC sun gano zargin alaka tsakanin Ahmadinejad da Isra'ila lamarin da ya tayar da hankali.
Asali: Legit.ng

