‘Abin da Habila da Ta Mutu a Gidan Minista Ta Fada wa Saurayinta kafin Ta Rasu’

‘Abin da Habila da Ta Mutu a Gidan Minista Ta Fada wa Saurayinta kafin Ta Rasu’

  • Ministan ayyuka, Dave Umahi ya yi karin haske kan mutuwar marigayiya Mary Habila bayan zarge-zarge
  • Umahi ya ce Habila ma'aikaciyar jinya ce mai rajista, ba likitar motsa jiki ba, kuma ta yi jinya a Turkiyya tare da iyalansa
  • Ministan ya buƙaci a yi gwajin gawar Habila, a mayar da bincike Abuja, tare da binciken bayanan kiran waya domin gano gaskiyar rasuwarta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi, ya bayyana bayanan tattaunawar ƙarshe tsakanin marigayiya Mary Habila da saurayinta.

Ministan ya bayyana cewa ta roƙe shi kada ya katse wayar kafin rasuwarta wanda ya zama shi ne kalamanta na karshe.

Umahi ya fadi silar mutuwar Habila
Marigayiya Mary Habila da Ministan Ayyuka, Dave Umahi. Hoto: @Pharmacio001, @realdaveumahi.
Source: Twitter

Martanin ministan ayyuka kan mutuwar Habila

Umahi ya yi martani kan mutuwar ma'aikaciyar Jami'ar Kiwon Lafiya ta Tarayya, inda ya musanta duk zargin da ke danganta shi ko gidansa da lamarin, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Umahi: A karshe ministan Tinubu da aka tsinci gawar budurwa a gidansa ya fadi abin da ya faru

Ya ce Habila ta kasance kamar 'yarsa, domin ta rayu tare da iyalansa tsawon shekaru uku, kuma ya san ta sosai.

A cewarsa, Habila ma'aikaciyar jinya ce mai rajista, ba likitar motsa jiki ba kamar yadda wasu rahotanni suka bayyana.

Ya ce tana fama da rashin lafiya kuma tana karɓar magani a wani asibiti da ke Turkiyya, inda iyalansa suka riƙa biyan kuɗin jinyarta.

Umahi ya fadi alakarsa da marigayiya Habila
Ministan Ayyuka a Najeriya, Dave Umahi. Hoto: Federal Ministry of Works.
Source: Twitter

Wayar da Habila ta yi da saurayinta

Umahi ya ce kafin rasuwarta, Habila ta kira saurayinta ta sanar da shi cewa jini yana zuba daga hancinta ba tare da tsayawa ba.

Ya ce saurayin ya shawarce ta da ta sanar da mutane halin da take ciki, sannan ya ce zai katse wayar saboda yana ganin ci gaba da magana zai ƙara matsalar.

Sai dai Habila ta roƙe shi da kalmar, "Kada ka katse wayar." Daga baya ya katse kiran, sannan bayan kusan mintuna uku da ya sake kiranta, ba ta amsa ba.

Ministan ya ce tun da safiyar ranar Habila ta sanar da saurayinta cewa za ta shiga wanka, kuma daga baya mutane suka fasa ƙofar ɗakinta bayan ta daina amsawa, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Mary Habila: Sababbin bayanai sun fito kan mutuwar budurwa a gidan Ministan Tinubu

A cewarsa, an tarar da famfon ruwa yana gudana, yayin da ya ƙara cewa ta yi jinyar ƙarshe ranar 5 ga Afrilu da kuɗinta ya kai kusan Naira miliyan 2.2, wanda shi ya biya.

Umahi ya ce ba ya zargin an aikata wani laifi, yana mai cewa Habila da wata ma'aikaciyar lafiya suna zaune ne a gidan baƙi da ke nesa da inda yake.

Habila: Yan sanda sun bukaci yin bincike

An ji cewa rundunar 'yan sanda ta jihar Ebonyi ta bukaci a gudanar da binciken gawa bayan an sami gawar Mary Habila, mai shekaru 26, a gidan Ministan Ayyuka, David Umahi.

Binciken farko ya nuna cewa Habila tana cikin tawagar ma'aikatan lafiya da suka raka Umahi zuwa gidansa, inda ta rasu a wani daki da ke cikin gidan ministan.

Iyalan Mary Habila sun ki amincewa da gudanar da binciken gawar, amma 'yan sanda sun dage cewa dole ne a yi shi domin gano hakikanin musabbabin mutuwarta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.