‘Yan PDP da Masoyan Ortom su na murnar samun nasara a kotun koli

‘Yan PDP da Masoyan Ortom su na murnar samun nasara a kotun koli

Magoya bayan jam’iyyar PDP a jihar Benuwai da kuma na gwamna Samuel Ortom sun fito kan titi su na murna da nasarar da su ka samu a kotun koli.

An ga wasu daga cikin Masoyan PDP da na Mai girma gwamnan na Benuwai su na wake-waken murna tare da rawa a kan titi saboda tsabar farin ciki.

Rahotanni da su ka zo mana daga jaridar Daily Trust sun bayyana cewa Masoyan gwamna da jam’iyya mai-ci sun ta tika rawa har gidan gwamnati.

A daidai wannan lokaci kuma an samu wadanda su ka yi tatul a wuraren shaye-shaye saboda nuna farin cikinsu na ganin Samuel Ortom ya sake nasara.

Wani daga cikin Masoyan gwamnan ya shaidawa Jaridar cewa wannan nasara ta masu dadi domin sun doke Jam’iyyar APC a duka kotun da aka shiga.

KU KARANTA: Ficewar Bichi daga PDP ba zai yi mana komai ba - Sakataren jam'iyya

‘Yan PDP da Masoyan Ortom su na murnar samun nasara a kotun koli
Gwamna Ortom na Jam’iyyar PDP ya yi nasara a kotun koli
Asali: Depositphotos

Bayan nasarar da jam’iyyar PDP da ta samu a zaben da aka yi a bara, Alkalai sun ba ta gaskiya a shari’ar da aka yi tun daga kotun sauraron karar zabe.

A Ranar 20 ga Watan Junairun 2020 ne kotun koli ta yanke hukunci game da shari’ar zaben Benuwai inda ta tabbatar cewa PDP ce ta lashe zabe.

Farfesa Jerry Agada wanda ya na cikin na-kusa da gwamnati, ya yi magana bayan hukuncin kotun koli, ya na ma cewa wannan shine zabin al’umma.

“A matsayina na Dattijo ba na sa ran ganin komai face nasarar jajirtaccen gwamnanmu, saboda nasarar da ya samu a kotun zabe da manyan kotun kasar.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel