Faston Katolika ya fada hannun masu garkuwa da mutane a Jihar Benuwai

Faston Katolika ya fada hannun masu garkuwa da mutane a Jihar Benuwai

Mun samu labari cewa wani fitaccen Fasto da ke Garin Otukpo, David Echioda, ya shiga hannun Miyagun masu garkuwa da mutane a karshen makon da ya wuce.

A jiya Ranar Litinin ne Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton sace wannan Bawan Allah a Garin Alan-Akpa da ke cikin karamar hukumar Otukpo a jihar Benuwai.

Rahotannin sun bayyana cewa an yi gaba da Faston ne a lokacin da ya ke dawowa daga Garin Utonkon a karamar hukumar Ado, inda ya halarci wani gangami.

Babban malamin katolika ya gamu da wannan rashin sa’a ne a Ranar Lahadi da rana sa'ilin da wadannan ‘Yan bindiga su ka far masa kan titi yayin da ya ke tafiya.

Ainihi Rabaren David Echioda mutumin Garin Oshugbudu ne a Yankin Agatu. Amma wannan Faston ya na aiki a wani coci da ke Ochobo, karamar hukumar Ohimini.

KU KARANTA: Aminu Aliyu: Shugaba Buhari ya aikawa mutane Jigawa ta'aziyya

Faston Katolika ya fada hannun masu garkuwa da mutane a Jihar Benuwai

'Yan Sanda su na bincike game da Faston da aka sace a Jihar Benuwai
Source: UGC

Wadanda su ka sace Shehin Malamin Mabiyan Katolika na addinin Kirista, sun dauke wayar salularsa bayan sun kama shi kamar yadda mu ka samu labari a jiya.

Wani Bawan Allah ya shaidawa ‘Yan jarida cewa ‘Yan bindigan sun tursasawa wani ‘Dan acaba da tsautsayi ta rutsa da shi ya zama masu ‘Dan jagora daga motar Faston.

“A lokacin da ‘Dan Acaban ya ke kokarin gyara babur dinsa a daji ne ya samu ya tsare. Wannan ‘Dan Acaba ne ya dawo ya sanar da cewa wasu sun dauke Faston a hanya.”

Shaidan ya bayyana cewa an sanar da Bishof Michael Apochi wannan lamari ne a Ranar. Sai dai har yanzu ‘Yan bindigan tuntubi kowa domin a biya kudin fansar sa ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel