Yansanda 2 sun bace, mutane 9 sun mutu a wani sabon rikici daya barke a jahar Benuwe

Yansanda 2 sun bace, mutane 9 sun mutu a wani sabon rikici daya barke a jahar Benuwe

Akalla mutane 9 ne suka gamu da ajalinsu da sanyin safiyar Laraba, 8 ga watan Afrilu sakamakon barkewar wata sabuwar rikici data kaure tsakanin kabilun Tibi da Jukun a karamar hukumar Ukum ta jahar Benuwe.

Punch ta ruwaito da farko dai an fara kashe mutane 3 a kauyen Jootar dake kan iyakar jahar Benuwe da Taraba, sai kuma wasu mutane shida da aka kashe a kauyen Mbamena na jahar Benuwe daga cikinsu har da wata mata mai shayarwa.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari za ta mika matatun man fetir ga wata kamfani mai zaman kanta

Yansanda 2 sun bace, mutane 9 sun mutu a wani sabon rikici daya barke a jahar Benuwe
Yansanda 2 sun bace, mutane 9 sun mutu a wani sabon rikici daya barke a jahar Benuwe
Asali: Getty Images

Rahotanni sun bayyana harin farko dai ya faru ne a lokacin da yan kabilun Jukun suka far ma kauyen Jootar, yayin da su kuma mayakan kabilar Tibi daga garin Tongov suka kaddamar da harin ramuwar gayya a Mbamena.

An ruwaito ko a kwanaki uku da suka gabata sai da wadannan mayakan Tibi dake karkashin ikon Ujoondo suka kai hari a garin Katsin-Ala inda suka kashe mutum daya. Amma a harin da Jukunawa suka kai Jootar kuwa, wata majiya ta ce da misalin karfe 4 na dare suka kai harin.

Majiyar ta kara da cewa baya ga kashe mutane 3, sun kuma kona fiye da gidajen Tibabe 200 a harin da suka kwashe tsawon awanni uku suka tafka barna tare da cin karensu babu babbaka ba tare da wani ya kalubalance su ba.

Shugaban karamar hukumar Ukum, Tortyokaa Ibellogo ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace an kashe mutane shida a hare hare biyu, amma ya daura laifin kisan a kan mayakan kabilun Jukun.

“A iya sani na wannan rikici ne tsakanin Jukunawa da Tibabe a jahar Taraba, don haka babu ruwan jahar Benuwe a ciki, saboda muma a nan muna da Jukunawa a Abintse, Wurukum da Makurdi, amma babu rikici tsakaninmu, muna zaman lafiya.

“Da wannan nake kira ga babban sufetan Yansanda, shugaban rundunar Sojan kasa da shugaban kasa su shigo cikin wannan matsalar kafin ta wuce gona da iri, saboda a yanzu muna fama da matsalar COVID-19 ne.” Inji shi.

A nasa jawabin, kaakakin rundunar Yansandan jahar Benuwe, DSP Catherine Anne ya tabbatar da samun gawarwakin wasu mutane uku da ba’a tabbatar da ko su wanene ba a garin Jooter.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng