Manyan jami’an gwamnatin Benue da Taraba sun isa Nasarawa domin tattauna rashin tsaro
- Manyan jami’an gwamnati daga jihohin Benue da Taraba a ranar Talata, 14 ga watan Afrilu sun isa jahar Nasarawa domin ganawa kan rashin tsaro a yankin
- Mataimakin gwamnan jahar Benue, Mista Benson Abopnu da takwaransa na jahar Taraba, Alhaji Haruna Manu, ne suka jagorancin tawagarsu zuwa wajen taron
- Shugabannin siyasa, sarakunan gargajiya da kungiyoyin addini, da sauransu ma za su halarci taron ganawar, ana kuma sanya ran za a kulla yarjejeniya a karshe
Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa manyan jami’an gwamnati daga jihohin Benue da Taraba a ranar Talata, 14 ga watan Afrilu sun isa jahar Nasarawa domin ganawa kan rashin tsaro a yankin.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mataimakin gwamnan jahar Benue, Mista Benson Abopnu da takwaransa na jahar Taraba, Alhaji Haruna Manu, ne suka jagorancin tawagarsu zuwa wajen taron.

Asali: UGC
An tattaro cewa an kira taron gaggawan ne ta bangaren gwamnan jahar Nasarawa , Abdullahi Sule, domin tattauna hanyoyin magance rashin tsaro a yankin arewa ta tsakiya.
An kuma ruwaito cewa shugabannin siyasa, sarakunan gargajiya da kungiyoyin addini, da sauransu ma za su halarci taron ganawar.
Ana sanya ran kulla yarjejeniya a karshen taron.
KU KARANTA KUMA: Covid-19: Ganduje ya shiga rudani kan shawarar rufe Kano
A wani labari na daban, mun ji cewa akalla mutane 17 ne suka mutu yayin da jirgin yakin Najeriya ya jefa bamabamai a kauyen Sakotoku dake karamar hukumar Dambo ta jahar Borno, bisa kuskure.
Jaridar TheCable ta ruwaito wadanda suka mutu a wannan harin sune mata da kuma kananan yara, wanda suke wasa da zaman shan iska a karkashin wata bishiyar mangwaro.
Majiyoyi daga gidan Soja sun bayyana an jefa bamabaman ne bayan rundunar Sojan sama ta samu labarin taruwar yan Boko Haram a kauyen, don haka ta shirya musu luguden wuta.
Inda ya kamata a kai harin shi ne wani yanki a Korongilum dake makwabtaka da Sakotoku da kimanin nisan kilomita 12, a nan ne mayakan Boko Haram din suka taru.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng